Home / News / Zan Samar Da Ingantacciyar Kasuwar Cinikin Citta Ta Zamani A Jaba – Godfrey Gayya

Zan Samar Da Ingantacciyar Kasuwar Cinikin Citta Ta Zamani A Jaba – Godfrey Gayya

Zan Samar Da Ingantacciyar Kasuwar Cinikin Citta Ta Zamani A Jaba – Godfrey Gayya

Imrana Abdullahi

 

 

Mai neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar shugabancin karamar hukumar Jaba a Jihar Kaduna Honarabul Godfrey Gayya ya bayyana cewa idan ya lashe zabe zai gina katafariyar kasuwar cinikin Citta ta kasa da kasa a yankin karamar hukumarsa.

 

 

Tsohon dan majalisar tarayya wanda ya zama shugaban kwamitin wasanni na majalisar Honarabul Godfrey Gayya ya shaidawa manema labarai cewa bayan da aka mika ainihin batun a samar da dan takarar da zai tsaya shugaban karamar hukumar Jaba a yankin da ya fito nan take jama’a suka ce lallai sai shi ne zai tsaya ba wata tantama “ni kuma kasancewar ina da dimbin basira tare da kwarewar aiki tun daga mataki na kasa baki daya duk abin da mutane na suka ce in tsaya takara dole in amsa kiransu domin ba ni da wasu da suka wuce su don haka na karbi batun tsayawa takara kuma nasara a gare mu take kamar yadda kowa ya sani”.

 

 

Ya dai bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan fitowarsa daga dakin tantance yan takara na ofishin jam’iyyar PDP a Kaduna.

 

 

Ya ce hakika tsayawarsa wannan takara na da fa’ida kwarai kasancewa zaka ga a matakin karamar hukuma masu yin shugabancin ana samun wadanda ba su da wata kwarewar aiki ko kadan don haka sai kawai ayi ta dama dama da sunan karamar hukuma.

Ya ci gaba da cewa za mu tsare dukiyar jama’a da zarar na zama shugaban karamar hukumar Jaba nan da yan kwanaki mai zuwa.

“Zan yi kokarin samar da wata babbar kasuwar kasa da kasa ta cinikin Citta (Ginger) kasancewa kowa ya san karamar hukumar Jaba wuri ne da ake samar da Cuttar da ta fi kowace kyau da inganci a duniya, za a samar da katafariyar kasuwar kasa da kasa da za ta rika ci a kullum dare da rana za a iya yin cinikayya da mutanen duniya baki daya”, inji Gogfrey Gayya.

Ya ce ya shiga wannan takara ne domin ya samar da kyakkyawan shugabanci ta yadda al’ummar karamar hukumar Jaba za su rarrabe tsakanin masu rawar jiki da sun ga dukiyar jama’a a matakin karamar hukuma da kuma wanda zai yi aikin daga darajar daukacin mutanen karamar hukumar baki daya.

“Kasancewata wanda ya zama dan majalisar tarayya a can baya ba zai hana ni yin abin da mutane na suka ce su na bukatar in yi ba tun da dai su ne ke zabe na a koda yaushe kuma yanzu sun ce ni kawai suka Sani sai na zama shugaban karamar hukumar Jaba a nan da yan kwanaki masu zuwa”.

Godfrey Gayya ya kuma bayyana gamsuwarsa da irin yadda aka gudanar da batun tantance yan takarar da za su tsaya neman shugabancin kananan hukumomi a karkashin PDP, inda ya bayyana lamarin da cewa abin sha’awa ne kwarai.

“Ai ba wata matsala kasancewar tun da wuri aka ba kowa ne dan takara tsarin jam’iyya kuma kowa ya karanta shi ya nazarci komai an kuma yi shawarar da ya dace ayi ta tuntuba tsakanin jama’a don haka babu wata matsala komai ya yi dai dai.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.