Home / Labarai / ZAN TALLAFAWA SARAKUNA SU TSIRA DA MUTUNCINSU – Dr Suleiman Shu’aibu Shinkafi

ZAN TALLAFAWA SARAKUNA SU TSIRA DA MUTUNCINSU – Dr Suleiman Shu’aibu Shinkafi

….Matsalar Tsaro Na Hana Gwamna Muhammadu Bello Matawalle, Bacci 
Daga Imrana Abdullahi
SAKAMAKON irin kokari da hakaza tare da don jama’a ya sa al’ummar karamar hukumar Shinkafi da ke cikin Jihar Zamfara suka yi tururuwa kwansu da kwarkwatarsu domin nuna Soyayya da kuma cikakken hadin kai da goyon baya ga dan takarar da ke neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar shugaban karamar hukumar Shinkafi.
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya ga dimbin kauna da Soyayya ga jama’ar karamar hukumar Shinkafi, da suka fito tarbarsa domin yi masa maraba da zuwa a matsayin dansu na hakika da suke kauna domin irin taimakon da yake yi masu a koda yaushe.
Tun da farko dai tawagar dan takarar shugaban karamar hukumar Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ta fara yada Zango ne a gidan maigirma Magajin garin Shinkafi, Alhaji Aliyu Ibrahim, a matsayinsa na uban al’umma da ke tare da su a koda yaushe.
Bayan yi wa Magajin gaisuwar bangirma an kuma gabatar da jawabai kamar dai irin yadda Dokta Suleiman Shu’aibu ke yi wa dimbin jama’ar da ke tsayar da shi a wurare daban daban saboda nuna kauna.
Dokta Suleiman Shu’aibu ya yi wa Magajin garin cikakken jawabin anin da ya sa shi amincewar da al’umma ke yi masa na ya fito neman wannan kujerar shugaban karamar hukumar Shinkafi.
“Na amince da irin kiraye kirayen da jama’a ke yi Mani na neman in fito takarar shugaban karamar hukumar Shinkafi ne domin yin hobbasa a ceto karamar hukumar daga halin da take ciki na tabarbarewar al’amura, wanda ya yi sanadiyyar matsalar tsaro, Tattalin arziki,Ilimi da kuma Noma da Kiwo wanda a can baya aka san karamar hukumar Shinkafi da yin fice a fannin Tattalin arziki da Noma da Kiwo ga kuma masu dimbin ilimi”.
Ya shaidawa Magajin garin Shinkafi tare da dimbin jama’arsa da ke tare da shi a lokacin cewa zai samar masu da tashar radiyo mai cin gajeren Zango na FM domin samun damar fadin albarkacin baki da kuma bayyanawa duniya irin hadin da suke ciki ta yadda za a samu dauki tun daga Jiha, kasa da sauran sassan duniya baki daya.
Ya kuma shaidawa dukkan yayan jam’iyyar APC cewa za a Jika su da abubuwan alkairi domin rayuwar jama’ar karamar hukumar ta inganta.
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya ci gaba da fadakarwa da cewa barin Sarakuna da aka yi ya haifar da dimbin matsalolin rashin tsaro da tabarbarewar al’amura a yankin.
“Saboda hak akwai kyakkyawan shirin da ake da shi na inganta harkokin dukkan bangaren masarautu baki daya a kowane irin mataki, wanda hakan zai taimaka wajen samar da ci gaba”.
Dokta Suleiman Shinkafi, ya shaidawa jama’ar Shinkafin cewa Gwamnan Jihar Zamfara baya Bacci domin kokarin magance matsalolin da ake ciki, a ko’ina a fadin Jihar da kasa baki daya.
Ya ce Mani “da zai samu wanda zai dauke wannan matsalar tsaron to da na bashi Gwamna. Gwamna baya Bacci saboda matsalar tsaro
Dokta Suleiman ya kuma bayar da tabbacin cewa “Ba za mu kunyata da Gwamna a Shinkafi ba, saboda haka muke yin kira ga daukacin al’umma da su bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamnan Matawalle, Gwamnatinsa da jam’iyyar APC domin a samu kwalliya ta biya kudin sabulu, wato ayyukan alkairin da mai girma gwamna ya kudirta su tabbata a karamar hukumar Shinkafi da Jihar baki daya”.
Sai dai Gwamnati na fadakar da jama’a cewa ya dace kowa ya Sani Jiha, kananan hukumomi ba su samar da  kudin shigar azo a gani, saboda haka dan abin da Gwamnatin Jiha ke samu daga daunin kason wata- wata ana amfani da shi ne wajen biyan Albashi,fansho, da sauran biyan abubuwa daban daban da Gwamnati ke yi
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya kuma bayar da wani albashin ga jama’a cewa “Za a fitar da wadansu mukamai da nade-  nade da yawa a wannan watan ga al’umma kuma Shinkafi na ciki domin akwai na ta kason mai tsoka da Gwamnan ya tanadar.

About andiya

Check Also

NASCON grows turnover by 37%, assures Shareholders of Continuous Growth, Value Creation

NASCON Allied Industries Plc has assured its shareholders of continuous growth and value creation in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.