Home / News / Zan Yi Kokarin Warware Matsalar Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Kaduna

Zan Yi Kokarin Warware Matsalar Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Kaduna

Alhaji Abba Anas Adamu, tsohon dalibi kuma tsohon Malami a makarantar Kwalejin kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin tarayya  da ke Kaduna wadannan na cikin manyan dalilan da suka bashi damar samun nasarar lashe zaben kungiyar tsofaffin daliban Kwalejin da aka yi dakin taron  kwalejin a kaduna, ga dai yadda Tattaunawar ta kasance da wakilinmu Mustapha Imrana Abdullahi. Ayi karatu lafiya.
Gashi ka lashe zaben kungiyar tsofaffin daliban Kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna shin wane irin tanaji aka yi domin ci gaban wannan kwalejin?
Abba Anas: Godiya ta tabbata ga Allah wanda shike da mulki kuma mai bayarwa ga wanda yaso, to mun yi wa Allah godiya da ya bamu wannan damar da muka roke shi.
Saboda haka ta inda zamu gode masa shi ne mu kamanta wajen aiwatar da aiki domin ci gaba, abin da yan kungiya ke bukata. Wannan kungiya ta tsofaffin dalibai ce da ke a ko ina da ina a fadin kasa baki daya saboda mun ma taba yin shugaban kasa a Nijeriya lokacin mulkin Soja mai girma Janar Abdussalamu Abubakar.
Muna da Gwamnoni da suke a kan mulki a yanzu muna kuma da tsofaffi da suka yi Gwamnonin, yan majalisar wakilai, sanatoci da sauransu da yawa a dukkan fannoni, da suka hada da kamfanoni sa masu sarauta da dai sauransu da dama.Saboda haka makarantar kwalejin kimiyya da fasaha ta kaduna wato ( kaduna polytechnic) na da manya manyan mutane da dama a wurare da yawa a Nijeriya da fadin duniya baki daya.
Saboda haka zamu yi amfani da wannan yawan mutanen na masu kudi, sarauta da kamfanoni mu hadu da su ido da ido mu gaya masu halin da makarantar ke ciki.
Ga dai makarantar ta girma amma bukatun da take da su ba su yi daidai da irin halin da take ciki ba. Abin da nake son in fadi shi ne ta girma amma abubuwan da za su kyautata rayuwa ta dan makaranta da malaman makaranta hakika ana karancinsu, na sani a fannin ilimi ba mu kadai muke da matsala ba amma idan aka yi la’akari da irin darajar mu yakamata ace abubuwan da muke da su sun wuce hakan saboda haka makarantar na da daraja da suna mai kyau.
A yanzu haka yawan daliban sun kusan dubu Talatin, amma idan aka duba inda suke kwanciya kasa da dubu hudu ne keda dakin kwanciya a cikin makarantar ga karancin gidajen Malaman makaranta ga karancin Ofisoshi saboda haka abin da zamu tunkara shi ne duk abin da ya shafi makarantar nan in dai zamu iya yin wani abu a kai ba shakka zamu yi domin a samu ingantaccen ci gaban da kowa ke fatar a samu.
Zamu tunkari manya manyan mutane da kananan manyan duk zamu nuna masu ga halin da makarantar ke ciki, kowane mutum tsohon dalibi daga inda yake shin zai iya ba sashen da ya yi karatu gudunmawa ko makarantar baki daya zai yi wa? Kowa ya zabi abin da zai iya yi wa makarantar nan kamar yadda masu karin magana ke cewa idan Giwa za ta kada itace to dole ne zomo zai karya ciyawa kowa ya yi abin da zai iya yi muga abin da Allah zai yi.
Ina son shaidawa jama’a cewa bamu ji dadin yadda muka samu kan mu ba a matsayin kungiya domin yakamata kungiyar ta fi haka, saboda ba daidai bane ace kungiyar nan sai a yanzu ake shirye shiryen kafa ta ba domin abubuwan da aka yi na baya a rushe suke saboda haka wannan Gwajin da zamu yi kwalliya za ta biya kudin sabulu.
Garkuwa: A matsayinka na zababben shugaban wannan kungiya ta tsofaffin dalibai, akwai kiraye kirayen da wadansu mutane ke yi musamman daga bangaren majalisar kasa cewa a mayar da wannan makaranta ta zama Jami’a.
Abba Anas: Ita harka ta karatu dai ni a ra ayina shi ne a canza ta ya zamana idan kayi karatun babbar Difiloma ta HND kayi digiri na biyu wato (masters) ko kayi digirin farko (BSC) kayi (masters) in ya zamanto wadanda suke bukatar tsayawa a matsayin matsakaitan ma’aikata sai su tsaya a ND ko HND kawai.
Wadanda kuma suke bukatar ci gaba da karatu sai su ci gaba misali makarantar nan ya dace idan da akwai abin da ya wuce ace digiri na uku wato (Phd) ya dace ace makarantar da kai. Amma sai ka gama nan sannan kaje wadansu makarantu kafin ka samu PhD to rashin samun irin wannan damar ke dakile mata girman da take da shi na shekaru 64 da kafuwa.
Ina ganin ko ABU Zariya da muke makwabtaka da ita sai dai ace sun tafi kafada da kafada in da akwai ci gaban da ake da shi. A kwanan baya ina karantawa a jarida cewa Jami’ar ABU Zariya na da Furofesa Furofesa wajen dubu shittin duk ita kadai sai mai binta jami’ar Ibadan dubu Arba’in sai kuma ta uku jami’ar Legas da ke da ko dubu Talatin ne? to a kwalejin kimiyya da fasaha ta Gwamnatin tarayya da ke  kaduna masu PhD nawa muke da su? Saboda haka ni dai a gani na in an bayar da damar a mayar jami a zai fi, domin akwai wadanda suke son yin karatu a nan kuma su ci gaba ba tare da sun fita ba sun je wata makaranta don haka indai akwai kayan aikin da za su yi ya dace a mayar kawai su tsaya a nan suyi karatunsu.
Mungode
Abba Anas: Nima na gode.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.