Home / Labarai / Zulum Ya Raba Wa Mutane 5,000 Kayan Abinci A Jere

Zulum Ya Raba Wa Mutane 5,000 Kayan Abinci A Jere

Zulum Ya Raba Wa Mutane 5,000 Kayan Abinci A Jere

Imrana Abdullahi

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Alhamis da ta gabata ya ziyarci wadansu al’ummomi uku da ke karamar hukumar Jere, inda ya duba rabon kayan abinci ga al’umma dubu 5,000 marasa galihu.

A lokacin ziyarar ya kuma bayar da umarnin aiwatar da wadansu ayyuka guda uku domin amfanin jama’a ya kuma kai ziyara ga inda sojoji suke aiwatar da aikin tsaro a yankin.

Zulum yaje Gongulong Lawanti, Khaddamari da Zabarmari, wadanda suka kasance su ne fitattun garuruwa a Jere.

Kayan abincin da Gwamna Zullum ya rabawa mutane kenan a wasu garuruwa Uku da ke Jere.

A Gongulong Lawanti, Gwamnan ya rabawa jama’a kayan abinci da dama ga iyalai dubu 4,000 mutane 1,000 kuma suka amfana a Khaddamari. Ya kuma halarci Zabarmari.

A dukkan wuraren da Gwamnan ya halarta ya samu ganawa da dimbin al’ummar garuruwan da ya ziyarta.

*3 new projects

A lokacin ziyarar Gwamna Zullum ya bayar da umarnin aiwatar da aiyuka uku da suka hada da aikin Gadar Zabarmari – Maiduguri.

Sai aikin cibiyar lafiya da kuma aikin kara samar da makaranta.

Gwamna Babagana Umara Zullum kenan lokacin da yake tafiya a cikin dimbin jama’arsa a Jere

Zulum ya kuma bayar da umarnin kammala aikin cibiyar lafiya ta Gongulong da aka fara tun lokacin mulkin tsohon Gwamna Sanata Kashim Shettima

A lokacin da ya ziyarci Jere, Gwamna Zullum ya ziyarci dakarun sojojin Nijeriya da suke aiki karkashin kamfani na 195 a Zabarmari, Khaddamari da Gongulong Lawanti domin kara masu kwarin Gwiwa.

Zulum ya kuma yi addu’ar neman Gafara ga dukkan sojoji da masu aikin Sa kai da suka rigamu gidan gaskiya a kokarin da suke na kare al’ummar Jihar Borno.

Ya kuma ba sojoji motar gudanar da zirga zirga domin tabbatar da taaron dukiya da lafiyar jama’a.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.