Home / News / GWAMNAN BAUCHI YA BUKACI ZABABBUN SHUWAGABANNIN KANANAN HUKUMOMI SU ZAMO KUSA DA AL’UMMA

GWAMNAN BAUCHI YA BUKACI ZABABBUN SHUWAGABANNIN KANANAN HUKUMOMI SU ZAMO KUSA DA AL’UMMA

GWAMNAN BAUCHI YA BUKACI ZABABBUN SHUWAGABANNIN KANANAN HUKUMOMI SU ZAMO KUSA DA AL’UMMA

Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir na jihar Bauchi ya bukaci sabbin Shuwagabannin kananan hukumomi guda 20 dasu zamo kusa da al’ummar su.

Gwamnan yabasu wannan shawarine a lokacin da ake bikin rantsar da sabbin Shuwagabannin kananan hukumominne a dakin taro na Gidan Gwamnatin jihar Bauchi.

Gwamna Bala Muhammad yace aiki da Zama kusa da al’umma dasuke kasa don kara samun karfin gwiwa daga al’ummar dasuke mazabunsu.

Gwamnan wadda yace suna da shekara biyu ne, yabayyana cewa cin Nasara ko akasin haka yarataya akan sauke nauyin da yake kankune yadda yadace.

Yabukacesu dasu bada himma wajen ganin sunyi anfani da abun da suke dashi ganin sunyi ayyuka da Tsare-tsare wadda zai Kara wa rayuwar al’ummar dasuke karkara inganci.

Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir ya bukacesu dasuyi Koyi da tsarin da Gwamnatinsa take dashi na ganin an tsaftace takardan biyan albashi don samun rara na ganin an aiwatar da ayyukan raya kasa da cigaba.

” Ina cike da farin ciki Ina Kuma maraba da zuwa wannan muhimmin taro mai tarihi, Na rantsar da basu rantsuwa na kama aiki wa Shuwagabannin kananan hukumomi wadda aka zaba da Mataimakansu wadda sukayi tsaya takara suka Kuma yi nasara a zaben daya gudana.

Wannan al’amari yashiga tarihi saboda rabon jihar da ayi zabe na kananan hukumomi shekara Sha biyu dasuka wuce.

” Amadadin nikaina Ina Godiya wa Allah daya bada dama wa Gwamantina na Siyasa na gudanar da zaben kananan hukumomi wadda na cikin alkauranmu na kanfen cewa zatayi zabe. Allah yabawa Kuma jam’iyyar mu ta PDP Nasara.

Gwamnan ya umurci sabbin Shuwagabannin kananan hukumomi dasu shiga cikin ayyuka wa al’ummah don tabbatar da zaman lafiya da tsaro don samun daman aiwatar da ayyukan da tsare-tsaren Gwamnati da shirye-shirye a Kauyuka.

” Ina tsamamnin zaku zamo masu Sa’ido a mazabunku Kan tsaro don taimakawa da rohoton duk wani abunda zai jawo nakasu wadda yasaba wa karya doka.

Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir ya rantsar da sabon mai rikon Shugaban Ma’aikatan jihar Bauchi, Alhaji Aliyu Jibo yabukaceshi da yataimakq wa Gwamnatin jiha don kawo sauyi kan aiki da kuma samun ingantacce da Kuma tsarin aiki.

Anasa jawabin Sabon Shugaban Karamar Hukumar Alkaleri , Alhaji Yusuf Garba wadda yayi magana amadadin sauran abokan aikinsa, yabayyana cewa a shirye suke dasuyi koyi da salon Shugabanci irin na Maigirma Gwamna Bala Muhammad.

Yusuf Garba yabayyana godiyarsu wa al’ummar jiha na Basu wannan damar dakuma karfin gwiwa dasuke dashi akansu.

 

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.