Home / Labarai / An Shawarci Yan Nijeriya Su Zama Masu Kaunar Yan Uwansu
Jihar Taraba na da arzikin Katako inda ake sarrafa shi wajen yin abubuwa daban daban har da kwanukan cin abinci kamar yadda zaku gani a wannan hoton

An Shawarci Yan Nijeriya Su Zama Masu Kaunar Yan Uwansu

Imrana Abdullahi
Wani mai kishin kasa da taimakon Al’umma a tarayyar Nijeriya, Alhaji Zayyanu Aliyu, ya shawarci mawadata da suke da Kumbar Susa da su hanzarta taimakawa marasa karfi da ke cikin Al’umma, da irin kayayyakin abinci da na amfanin yau da kullum.
 Kamar yadda ya bayyana cewa ba wani abin sha’awa ace mutum na cikin wadata, amma kuma sauran wadansu mutane na cikin matsalar talauci, to ina abin Burggewa a ciki.
Wannan kiran yazo ne a lokacin da duniya ke fuskantar matsalar cutar Korona bairus, da ta tagayyara tattalin arzikin duniya baki daya, wanda sakamakon hakan rayuwar mutane da yawa shiga cikin mawuyacin hali a duniya, mutanen kuma sun hada da na Nijeriya da na Sakkwato
“Hakika, wannan cuta da ake kira da Korona ta Jefa al’ummar Nijeriya a cikin matsanancin halin tattalin arzikin kasa da kuma nakasa tattalin arzikin jama’a baki daya kuma irin yadda ake daukar matakin rufe jihohi da garuruwa shima wani abin da ke haifar da Matsatsi ne ga al’umma.
Wannan yanayi ya Jefa da yawa daga cikin yan Nijeriya cikin mawuyacin halin da da yawansu ba su ma iya samun cin abinci sau daya a rana balantana kuma masu ciyar da Iyali.
Saboda haka ne, ” ya zama wajibi a taimakawa marasa karfin da ke cikin al’umma da kayan Tallafi irinsu abinci, abin sha da sauran kayan amfanin yau da kullum, kada masu hannu da shuni su bar abin sai Gwamnati, Sato matakan Gwamnati uku kawai za su taimakawa jama’a don haka muke cewa ba sai Gwamnati ba kawai.”
” Wannan wata fafutuka ce da ta rataya a wuyan dukkanmu a matsayinmu na masu hannu da shuni ko kuma a matsayin mu na wadanda za su iya taimakawa juna a tsakaninmu da musamman kayan abinci don haka ya zama wajibi dukkanmu mu taimaka.
” Yan Nijeriya mazauna kasashen waje suma ya dace su hada kansu domin kawowa yan uwansu dauki a Nijeriya”.
 Aliyu, ya kuma yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da suma su hanzarta tashi tsaye domin taimakawa jama’a su fita daga cikin halin kuncin da suke ciki.
Aliyu, ya kuma ci gaba da ankarar da masu karfi a cikin al’umma, kamfanoni da yan Nijeriya mazauna kasashen waje da su yi koyi da irin abin da shahararren dan kasuwa Alhaji Aliko Dangote yake yi da kuma abin da mai kamfanin BuA duk baki daya suke yi na taimakawa marasa karfi musamman ma irin yadda suke yi wa Kano a wannan lokacin kalubale.
” Ba wai sai mutum ya Tara wata dimbin dukiya da zai iya taimakawa marasa shi ba a’a koda mutum yana da kwanon abinci daya zai taimaki wanda bashi da shi a cikin jama’a, zaka iya taimakawa mutum da kwanon abinci ko masara ko Dawa da sauran kayan abinci”.
” Irin wannan ne ke faruwa a kasashe kamar na tarayyar Turai, Amurka, da yankin Asiya da kuma kasashen Larabawa, to saboda me mu zamu kasance daban?”
Alyu Ya kuma bayyana bukatar da ke akwai ga masu kudi da sauran jama’a, Kamfanoni da su tallafawa mabukata da kayan amfani irin su Magunguna Magunguna sauran kayan amfanin da nufin yaki da matsalar Korona bairus.
 Aliyu, ya kuma yi kira ga yan majalisar kasa da suka fito daga Jihar Sakkwato da masu rile da muhimman mukamai a Gwamnatin tarayya da su tuntubi Gwamnatin tarayya da azo domin gudanar da bincike kan abin da ke kawo mace macen da ake samu a garin Sakkwato da kewaye da kuma wasu sassan Jihar.
Yin hakan zai taimaka a san musabbabin mutuwar mutane da ake samu a kusan kowace rana domin a gano ko akwai wata alaka da cutar Covid -19 da ake kira da Korona.
” Sakamakon zai ba Gwamnati da sauran hukumomin lafiya na Nijeriya da na kasa da kasa su yi abin da ya dace domin kare lafiya da dukiyoyin jama’a,” Aliyu ya jaddada.
Aliyu Ya kara da yin addu’ar Allah ya gafarta wa wadanda suka mutu, marasa lafiya kuma da suka kamu da wannan cutar Allah ya kawo masu sauki, Allah kuma ya Italian mamatan hakurin jure rashin da suka yi.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.