Home / News / 2021: Jigon PRP Ya Bayyana Matsalolin Siyasar Nijeriya

2021: Jigon PRP Ya Bayyana Matsalolin Siyasar Nijeriya

…Ya Karbi Bakuncin Musilmi, Kirista A ranar Sabuwar Shekarar 2021
Mustapha Imrana Abdullahi
Mataimakin shugaban jam’iyyar ceton al’umma PRP kuma shugaban shiyyar ta II, St Kamven Enoch Nannim, ya bayyana matsalar son zuciya da hadama cewa shi ne ke zama babbar matsalar  yan siyasar Nijeriya.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin al’ummar Musulmi da Kirista tare da yan jarida da kuma abokai da masu fatan alkairi  a gidansa da suka kai masa ziyarar barka da murnar shiga sabuwar shekarar 2021 a gidansa da ke Sabon Tasha, cikin garin Kaduna.
Ya bayyana cewa ya yi ko yi da irin yadda ya ga ana yi ne daga magabatan da suka gabata kafin shi, a kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin Juna, domin tafiya tare da kowa ta yadda za a samar da ci gaba.
Jigon na PRP, St Enoch da ya karbi bakuncin dimbin al’ummar Musulmi da Kirista a ranar farko ta sabuwar shekarar 2021 a cikin gidansa.
”Abubuwa da yawa sun zo kuma sun wuce, kamar yadda muka zauna a nan muna yin magana kai tsaye ta hanyar tattaunawa da Juna ba tare da wata tangarda ba, balantana batun addini ko kabilanci ba wannan nankara mana samun dankon zumunci da Kaunar juna da ke kawo hadin kai. Mun tattauna a kan abubuwa da dama da nufin tinatarwa kada mu bari wani ko wasu su karkatar da mu a wannan shekarar ta 2021 da dai sauran al’amura baki daya”. Yana mai jaddada hakan.
Jigon jam’iyyar PRP ya shawarci yan siyasa da su yi ko yi da kyakkyawar aniya da jam’iyyar PRP take da shi a rika yin dukkan abin da za a yi domin Allah da niyyar inganta rayuwar jama’a a ko yaushe wanda hakan ne zai sa a samu zaman lafiya a tsakanin al’umma da nufin kawar da matsalar tsaro, da suka hada da batun satar mutane da cin hanci da karbar rashawa a cikin wannan shekarar ta 2021.
 Kamar yadda ya jaddada cewa babu wani amfani da wani ko wasu za su samu ba tare da zaman lafiya da Kaunar Juna ba, inda ya kara fadakar da jama’a cewa samun abin alatun duniya da duk wata kawar duniya da samun ci gaba ba zai samu ba a cikin hali irin na rashin zaman lafiya musamman a cikin yanayin kinci da rashin tsaron Dukiya da rayuwar al’umma.

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.