Home / News / 2023 :An Kai El- Rufa’I Kotu

2023 :An Kai El- Rufa’I Kotu

Imrana Abdullahi
Sakamakon irin tsananin matsuwar da wadansu mutane suka yi domin ganin Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya tsaya takarar neman shugabancin Nijeriya a shekarar 2023 yasa wadansu mutane suka kai shi kotu.
Su dai wadanda suka kai shi kotun sun ce sun yi hakan ne domin kotun ta tilasta masa ya tsaya takarar a shekarar 2023.
Garkuwa Ibrahim Babuga shugaban kungiyar fafutukar ganin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ya tsaya takara a 2023 ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da gidan rediyon Jihar Kaduna KSMC cikin shirin siyasa “Bakin Zaren”.
Alhaji Ibrahim Babuga ya ce tuni har an shiga kotun kuma an yi zaman sauraren shari’ar karo biyu kuma nan da sati daya za a shiga shari’a zaman kotun na uku.
“Muna nan muna ta yin addu’o’in Alkunutu domin rokon Allah yasa Gwamna Nasiru El- Rufa’i ya amsa zai tsaya takarar kujerar shugaban kasa saboda cikar kamala da nagartar da Gwamnan yake da ita”.
Ya ci gaba da cewa ” Ko a cikin yayan mutum akwai wanda mutum zai iya ba shi amana a kan wadansu al’amura don haka muka ga ya dace sai Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ya tsaya takara domin ci gaba da bayar da gudunmawarsa wajen ciyar da kasa gaba”, inji Ibrahim Babuga.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.