Home / News / 2023: Dattawa Arewa Sun Ki Amincewa Da Batun Cire Ayu Daga Shugabanci PDP…

2023: Dattawa Arewa Sun Ki Amincewa Da Batun Cire Ayu Daga Shugabanci PDP…

Hadin Kai Don Lashe Zabe Yafi Komi Muhimmnaci
– Yan Kudu Na Son Hargitsa Makomar PDP
Wadansu yan kungiyar fafutukar kare muradin arewacin Najeriya karkashin wasu Dattawan jam’iyyar PDP da ke arewacin Najeriya sun bayar da shawara ga sauran Dattawan jam’iyyar da ke wasu yankunan kasar musamman ma wadanda suka fito daga Kudancin kasar domin kada su bari wani ya yi amfani da su wajen zafafa harkokin siyasa Wanda hakan ka iya haifar da matsala ga jam’iyyar a lokacin zaben 2023 mai zuwa.
 Bayanin hakan ma kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da da hannun Dokta Nasiru Aliyu Sadauki, babban Ko- odineta na kasa domin hada kan dattawan yayan jam’iyyar PDP domin hadin kai.
A cewar wadannan Dattawan,da akwai hanyoyin da za a bi na zaman lafiya domin warware irin yadda ake ta yin maganganu game da batun cire shugaban jam’iyyar PDP Dokta Iyorchia Ayu, domin a samu zaman lafiya kasancewar akwai bukatar a mayar da wuka cikin kube da nufin ci gaban PDP, a hada kai kafin lokacin kaddamar da abban Yakin neman zaben dan takarar shugabancin kasa Atiku/Okowa
Kamar yadda ko- odinetan kungiyar na kasa Dokta Nasiru Aliyu Sadauki, ya bayyana a wata takardar sanarwa bayan kammala taro da mambobin kungiyar mutane  Arewa da suka hada da masu ruwa da tsaki da kuma masu yi wa harkar fatan alkairi tun daga shekarar “2022 – 2023 da suka hada da masu wayar da kan al’umma domin samun nasarar PDP, da ke fadakarwa a zabi Atiku/ Okowa ta hanyar kungiyoyin taimakawa masu fafutukar a Kaduna.
Duk wannan an yi shi ne da nufin samun kara karfin Gwiwar samun fadakarwa da wayar da kan mutane nan take a wasu Jihohin arewacin Najeriya.
Kamar yadda Sadauki, Jagororin jam’iyyar ya dace ne su fuskanci muhimman al’amura da suka hada da batun tattalin arzikin kasa, lamarin tsaro, Talauci,halin da Ilimi ke ciki da sauran wasu kalubalen da ke tattare da batun hadin kan kasa a matsayin mu da al’umma daya a madadin yin wasu batutuwan cire shugaban jam’iyyar PDP.
Akwai wadansu batutuwan a kasa da ke bukatar sai shugabanni sun sadaukar da kai, su kuma lalubo hanyoyin magance su a Najeriya. Ba wani dan jam’iyya mai hankali da zai rika zuzuta batun a cire Ayu daga shugabancin PDP, musamman a wannan lokacin da ake bukatar samun hadi kai tsakanin Juna ta yadda za a samu fahimtar Juna a jam’iyya.
Yan Najeriya sun Gaji da yin irin wannan wasan yara daga wasu masu kunnen kashi da suka yi wani rukuni wai su ne masu ilimi tare da wayewa a kasa. Bari kawai mu fuskanci wasu batutuwa mu kuma rabu da wasu rukunin yan siyasa da suke kokarin kawai jama’a su tausaya masu fiye da kokarin yin aiki domin sake Gina Kasa.
A kowace rana muna tashi da samun labaran cewa wasu al’amura sun faru a kasa kamar KISAN mutane, satar jama’a na mutanenmu yan Najeriya da suka hada da Maza da Mata manya da yara, amma kuma Gwamnatin APC ta kasa yin komai wajen kawo karshen matsalar. Abin mamakin sai kuma kawai jam’iyyar mu ta na ta magana a kan Ayu, ” dole sai Ayu ya ta fi” domin wai “Kudu Kudu za su amince ba” duk da cewa za a iya warware wadannan abubuwa cikin ruwan sanyi.
Rikicin jam’iyyar PDP wani lamari ne da aka kirkire shi, da nufin Rusa duk wani kyakkyawan shiri da za a samar sahihan hanyoyin ci gaban jam’iyya karkashin jagorancin Ayu. Masu kokarin haifar da wannan matsalar ta rashin hadin kai da ci gaban yayan jam’iyyar PDP duk su na yin hakan me da nufin haifar da matsala domin yan Najeriya su ga cewa babu wata jam’iyyar da za su goyawa baya sai APC a zabe na kasa da sauran zabubbuka baki daya.
Muna yin kira ga masu goyon bayan jam’iyyar PDP a ciki da wajen Najeriya da su hada kansu domin goya wa shugabancin PDP baya karkashin jagorancin Dokta Iyorchia Ayu da a hada kai baki daya a ceto lamarin ta yadda za a samu damar sake gina Najeriya daga irin Barnar da APC ta aikata a fadin kasa baki daya.
Batun rashin kokarin Gwamnati karkashin APC na warware matsalar yajin aikin kungiyar malaman jami’o’I kawai wannan dalili ne da zai Sanya a fara ganin cewa ya dace ayi aiki tare da shugabancin jam’iyyar PDP na kasa domin kawar da APC daga kan karagar mulki a shekarar 2023.
Saboda haka muke bayar da shawara ga babbar majalisar da ke yi wa PDP jagoranci karkashin Ayu, da su hanzarta fara yin aikin kokarin hada kan yayan jam’iyya da nufin samun karfin Gwiwar nasara a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.