Home / News / 2023: Saukar Ayu Da ga Shugabancin PDP, Zai Kasance Fitina Ga Atiku

2023: Saukar Ayu Da ga Shugabancin PDP, Zai Kasance Fitina Ga Atiku

 

 

 

Masu Neman Haka, Makiya Cin Nasarar PDP Ne

 

 

Haddadiyar Majalisar Matasan PDP ta kasa yankin Arewa maso yamma ta baiyana rashin amincewa tare da yin fatali da duk wani shiri don neman a tursasa ma Shugaban jam’iyyar PDP na Kasa Dr Iyorchia Ayu da ya aje mukamin sa da sunan sulhuntawa da Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da mutanen.

 

 

Shugaban Majalisar Abdullahi Idris Maikudi ya baiyana haka a garin Burnin Kebbi a yau Talata bayan kammala taro na mussaman dangane da yanayi da matsaloli da ke fuskantar PDP a Arewa maso yamma.

 

Majalisar ta yi kakkausan suka dangane da yadda wasu tsiraru a cikin jam’iyyar suke kokarin mayar da hannun agogo baya ga samar da ci gaba, hadin kai da nasara PDP a zaben 2023.

 

“Duk dan PDP mai son nasara ko tunanin ci gaba, ba zai kawo zancen a cire ko shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu yayi murabus ba; neman haka ko kadan baya daga cikin abin da ya dace ga zaman lafiya da fahimtar juna a cikin PDP.

 

 

“Yan Arewa ba zancen Ayu bane a gabansu, mun fi damuwa da samun nasara PDP don ceto yankin mu na Arewa da aka kassara aka mayar dashi a matsayin wuri na kisan juna, garkuwa da kuma lallata masa daraja”.

 

Alhaji Abdullahi ya ce; a Arewa matsalar tsaro, lallacewar tarbiyya da rikicin ASUU da tattalin arziki ya fi zama abin damuwa da zancen wai akwai wasu da ke son ala dole sai sun cire Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa.

 

Ya nemi al’ummar arewa dasu ci gaba da baiwa PDP da yan takarar jam’iyyar goyon baya har sure lashe zabe a maimakon mayar da hankali ga ga surutan da basu da amfani.

Ya ce, za su ci gaba da ilmantar da jama’a tun daga runfar zabe har zuwa mazabu da kananan hukumomin mulki a kan dacewar zaben Atiku Abubakar da sauran yan takarar jam’iyyar baki daya.

About andiya

Check Also

The Daily Hug For Appreciation 2023

The daily hug for 28/11/23 is this appreciation of an echo shared by my dear …

Leave a Reply

Your email address will not be published.