Home / Labarai / An Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Samar Da Tagwayan Hanyoyi A Garin Potiskum

An Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Samar Da Tagwayan Hanyoyi A Garin Potiskum

 

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

 

 

Al’ummar Karamar Hukumar Potiskum da ke jihar Yobe sun bukaci gwamnatin Tarayya da gwamnatin jihar Yobe da su hada hannu wuri guda domin samar da tagwayen hanyoyi daga Garin Adaya zuwa Babbar hanyar Jos, domin rage cunkoson ababen hawa da hadurra.

Wani jigo a Jam’iyyar APC Alhaji Ibrahim Adamu Gurgusku (Tafidan Tikau) ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da wakilinmu a garin Potiskum, Ya bayyana dalilin sa na neman gwamnatin tarayya karkashin Shugaban Kasa Muhammadu  Buhari da kuma taimakon gwamnatin jihar Yobe karkashin Gwamna Mai Mala Buni da su hada hanu guri guda domin aiwatar da aikin.

Alhaji Ibrahim, ya ce samar da tagwayan hanyoyi a wannan wurin abu ne da zai rage cunkoson ababben hawa tare da rage hadurra akan titunan ganin yadda manyan motocci ke wucewa zuwa garin Maiduguri daga garuruwan Legas, Enugu, Benin, Abuja dakuma Jos domin safarar kayayyaki.

Gurgusku da yake bayyana muhimancin hanyar musamman a ranakun kasuwar shanu, hatsi da kuma ranar laraba domin masu zuwa sayen dabobbi daga garuruwa daban-daban dake fadin kasar nan har ma da kasashen waje. Ya ce a lokutan da ake cin Kasuwa, samun wucewa da abin hawa yana matukar bada wahala mussamman idan rana tayi ko yamma. A wannan lokacin ne ake samun hadura tare da ke kai da kashe mutane.

Dan Siyasar ya kuma yabawa gwamnan Jihar Yobe Hon Mai Mala Buni bisa ga irin aiyukan da yake aiwatarwa a garin Potiskum wanda suka hada da samar da gidaje, Farfado da kamfanin sarrafa abincin Masara wato ( Flour and Feed Mills), Ma’aikatar sarrafa Kwanan rufi wato (Yobe State Aluminum Company) kasuwar zamani, hanyoyi a cikin gari, baiwa yaran ‘yan makaranta abinci kyauta, gine-ginan sabbin kananan asibitoci a karkara domin kula da marasa lafiya, ga kuma samar da wurin aje manyan motoci tare da samawa matasa kimanin dubu biyar aikinyi a ( Trailer park).

Alhaji Ibrahim, ya shawarci al’ummar jihar Yobe da su ci gaba da bayyana goyan bayansu ga gwamnatin jihar Karkashin jagorancin gwamna Hon Mai Mala Buni domin samar da karin hanyoyin raya kasa da kuma ciyar da jihar gaba domin amfanin jama’a.

Da ya ke tsokaci dangane da zaben shekara ta 2023,  kira ya yi ga ‘ya’yan jam’iyyar APC musamanma matasa da su tabbatar Sun mallaki katunan zabe wato Permanent Votes Registration Card PVC) wanda zai ba su damar zaben shugabannin da suke so a matsayin wakilansu.

Gurgusku, ya yi kira ga shuwagabanni, Malaman addinai, masu hanu da shuni da su yawaita gudanar da adu’o’i na musamman don samun zaman lafiya mai dorewa a kasan nan.

Daga nan ya shawarci magoyan bayan Jam’iyyar APC da su tabbatar sun zabi Dan takarar shugaban kasa wato Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.