IMRANA ABDULLAHI (NORTHERN NIGERIA)
Kotun daukaka kara da ke shiyyar Sakkwato a arewacin tarayyar Najeriya ta tabbatar da dan takarar Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP, a zabe mai zuwa na shekarar 2023 da za a yi a watan Fabrairu mai zuwa.
Alkalin kotun a halin yanzu ya jingine hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Gusau ta yi inda ta hana Dauda Lawal Dare tsayawa takarar Gwamnan.
Idan dai za a iya tunawa Injiniya Ibrahim Shehu daya daga cikin yan takarar Gwamnan ne ya kai karar Dauda Lawal bisa abin da ya kira an yi ba dai dai ba a wajen zaben fitar da dan takarar Gwamnan Jihar Zamfara a Jam’iyyar PDP.