….Zan Yi Bakin Kokari Na Wajen Kawo Ci Gaba
DAGA IMRANA ABDULLAHI
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma zababben Sanata karkashin jam’iyyar APC Abdul’azeez Abubakar Yari, ya bayyana cewa zai yi iyakar kokarinsa wajen kawo ci gaban kasa tare da al’ummarta baki daya.
“Kamar yadda na rika fadi a lokacin gangamin neman jama’a su zabe mu karkashin jam’iyyar APC cewa zan yi iyakar kokarina domin in ga an magance matsalar tsaron da ke addabar jama’a, saboda haka zan hada kai da Gwannatin tarayya wanda alhakin ta ne ta kawo wa al’umma ingantaccen tsaron lafiya da dukiyar jama’a. Amma a na mu bangaren lallai za mu yi kokarin ganin karshen lamarin, domin abu na farko da ya dace mutum ya yi shi ne ya tabbatar wa da jama’a tsaron lafiya tare da dukiyarsu wannan ya sa muka yi wa jama’a alkawarin hakan don haka za mu yi aiki kan jiki kan karfi wajen taimakon jama’a”.
Sanata Abdul’azeez Yari, ya kuma yi bayanin cewa akwai wani al’amarin da ya zama wajibi in ambace shi, shi ne ina yin kira ga dukkan daukacin jama’a da ke bangare na, domin dole ne in fayyace wannan,cewa akwai bangare. Amma duk da hakan ” ina yin kira a gare su da su fito ranar zabe domin zaben jam’iyyar APC Sak, domin na lura da cewa akwai wadansu abubuwan da suka faru a wadansu wurare, saboda idan ka na da Sanatoci da yan majalisun wakilai ya nuna cewa kana da kashi Talatin da Biyar ne kawai a cikin dari. Saboda haka Gwamnatin Jiha ce za ta fi kusa da jama’a da kuma ta san abin da suke ciki domin magance damuwarsu idan akwai, kuma akwai batun neman zabe a wadansu shekaru nan gaba masu zuwa don haka dukkan mutane na su fito ranar 11 ga Maris, cikin ikon Allah su zabi dukkan yan takarar APC”.
Kuma za mu ci gaba da fitowa domin wayarwa da jama’a kai har mu gamsar da su cewa ya dace su shigo cikin jam’iyyar APC kuma su zabi yan takarar ta a fadin Jihar Zamfara baki daya.
A game da lashe Zabensa da ya yi kuwa, sai ya yi wa Allah madaukakin Sarki godiya a bisa hakan, sai kuma abu na biyu shi ne ina godiya ga shakikan abokaina da suka bayar da lokacinsu duk da irin yadda ake cikin yanayin zafin rana don haka ina yi masu godiya kwarai domin Allah ne kawai zai iya biyansu, don haka ina tabbatar masu zan yi iyakar kokari na wajen tabbatar da ci gabansu.
“Hakika samun nasara ta wani al’amari ne daga Allah domin babu abin da mutum zai yi wa dan Adam ya samu damar abin da ke cikin zuciyarsa sai da ikon Allah”.
Yari ya ce suna saran samun nasara a zaben Gwamna da yan majalisu mai zuwa domin idan an lura ko a zabe na kasa da aka yi,duk an kama hanyar samun nasara, don haka jama’a sun San cewa su wayayyu ne saboda haka ya dace su yi zabe cikin wayewa. Don haka ne ma muka yi ta fadakar da jama’a cewa za mu yi maganin abin da ake ganin kura – kurai ne.
Kuma akwai wani abu guda cewa ” ni ba zan fadi abin da na san ba zai yuwu ba don haka ina tabbatar wa da jama’ar Jihar Zamfara cewa ni ina yin aiki ne ga jam’iyya ta APC kawai don haka nake yin alkawarin samar da ingantacciyar nasara da ci gaban al’umma baki daya.
Jama’a na ta tururuwa gidan zababben Sanata Abdul’azeez Abubakar Yari da ke garin Talatar Mafara domin taya shi murna da cin zabe Sanatan Zamfara ta Yamma, bisa abin da wadansu da muka zanta da su sun shaida mana cewa Sanata Abdul’azeez Yari mutum ne mai kokarin rikon jama’a ta hanyar inganta rayuwarsu don haka duk inda ya Dosa jama’a can suka yi.