Daga Imrana Abdullahi
Kwamared Gambo Ibrahin Tuge mai binciken kudi ne a matakin kasa na kungiyar direbobin Tankar Mai wato masu dakon man fetur ya yi kira da babbar murya ga Gwamnatin tarayya da a hanzarta lalubo wa al’ummar Najeriya da hanyoyin da za su samu saukin radadin cire tallafin mai da aka yi.
Kwamared Gambo Ibrahim Tuge, ya ce hakika ba su ji dadin cire wannan tallafin ba, ba kuma wai domin suna cikin tsarin ba ne sai domin irin halin tsananin matsin da Talakawa ke ciki ne kawai ke damuwarsu don lamarin abin tashin hankali ne kwarai matuka.
” Ba domin ko wani zai rasa wani abu ba saboda duk wanda Allah zai bashi wani abu ba mai iya hana wa sai ya samu daga Allah. Amma dai mu a zahiri muna ganin iron yadda abubuwan more rayuwa suka yi sama baki daya, musamman ga masara a wasu wuraren ta kai ga naira dubu Talatin da biyu zuwa da Tara saboda haka wannan abin tashin hankali ne da Talakawa za su ce ina za su Sanya kansu a wannan rayuwar.
Kuma bayan tashin farashin kayan abinci har yanzu kananan ma’aikata ba a ba su wani Albashi cikakke ba, da an yi wani tanadi da al’umma za su amfana da shi don an ce an cure gaba daya kowa ba zai samun damuwar hankalin da ba ko kadan. Amma mu damuwar mu ita ce talakawan kasa domin a koda yaushe muna cikin Talakawa koda yaushe kuma muna jin abin da ke gudana.
“Akwai wani a kauye da ya gaya Mani wata maganar da hankali na ya tashi da na ji kamar in yi kuka sai na tambaye shi yaya suke yi da halin rayuwa, sai ya ce idan a cikin kwana daya ko biyu sun samu Masara ko Dawa sai ayi Tuwon da za a yi kwanaki Uku ana cin Tuwon, sai na tambaye shi kamar yaya sai shi kuma ya ce idan suka dafa shi ya dahu za su Sanya shi a cikin Kula ta ajiye abinci sai suyi masa miya tashi ta musamman. Sai kuma idan Yamma ta yi sai suje su nemo Tafasa su kuma yi miya da ba kowa zai iya cin irin ta ba har ayi kwana uku ana ci, kaga wannan abin takaici ne da ban tsaro da ya kamata ayi tunaninsa a kasa kamar Najeriya da Allah ya yi wa arzikin Noma da albarkatun man fetur”, inji Tuge.
Da yake amsa tambaya a kan ina mafita game da lamarin mai? Sai ya kada baki ya ce a halin yanzu dai ba a cewa ga wata mafita a kusa kusa, domin me? Idan an duba lamarin Dalar Amurka da ake amfani da ita a sayo mai fetur a kasashen duniya irin yadda farashin ta yake a yanzu in dai ba Gwamnati ta yi masu tanadi na musamman ba to, nan gaba ma Dalar sai ta kai dari Bakwai ko Takwas, kuma idan an ke an sayo man sai ya kai ga naira dari shidda zuwa Bakwai wanda ba a fatan hakan. Kaga madadin Talaka ya ji dadi sai ya kara samun wahala kuma.
Saboda hakan mu Talakawa ne tunanin mu a koda yaushe muga me talaka za a yi masa ya samu saukin rayuwa da zai more dadin rayuwarsa domin idan ka duba sosai talaka baya samun wutar lantarki, haka ruwan sha haka ma abincin da zai ci duk baya samu, to, ina zamu saka kan mu yadda Najeriya keda dimbin jama’a da ake ganin ita ce ta daya a Afirka da muke jin dadin rayuwa sai kuma ace Talakawa na yin kuka a gidajen rediyo wani ya ce ya kwana bai ci abinci ba wani ma ya kwana biyu bai iya yin cefa ne ba wannan lamarin na cikin abin tashin hankali kwarai.
” Mu a iya sanin mu duk kasar da aka cire tallafi a duniya ana yin wani tanadi ga yan kasa domin a sauke masu radadin da ke damun su saboda haka ne muke fatan ita ma wannan Gwamnatin Allah ya bata ikon yi wa al’ummar Najeriya tanadin wadansu abubuwa na samun saukin radadin cire wannan tallafin, domin idan an duba hatta da Raza ko Magi duk sun yi sama a farashi to, ina talaka zai Sanya kansa don haka muke fatan Allah yasa hankalin Gwannati ya karkata a wannan wurin domin idan za ta yi rabon ta duba talakawan wadanda ya dace aba, ba masu kudi ba a kara wa Barno Dawaki ba kawai su mance da yayan Talakawa ba.