Home / Kasuwanci / Gwamna Dikko Radda Ya Bukaci Yan Kasuwa Su Saukakawa Jama’a

Gwamna Dikko Radda Ya Bukaci Yan Kasuwa Su Saukakawa Jama’a

Daga Imrana Abdullahi
Kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin addinai na Jihar Katsina Honarabul Ishaq Shehu Dabai ( Kadimul Islam na Jihar Katsina) ya yi kira da babbar murya ga dukkan daukacin yan kasuwa da su saukakawa jama’a a cikin kasuwancinsu.
Kwamishina Ishaq Dabai ya yi wannan kiran ne a lokacin wani babban taron da Ma’aikatar kula da harkokin addinai ta kira Malamai daga kowa ne bangare a karon farko a Jihar Katsina.
Kwamishina Dabai ya ce Gwamnan Jihar Katsina ne Dokta Dikko Umar Radda ya bayar da umarnin a kira wannan taron na Malaman addini a kowa ne bangare domin su fadakar da yan kasuwa bukatar da ke akwai na su saukaka wa al’umma a kan farashin da suke sayar da kayan sayarwarsu.
Saboda an lura da akwai wadansu da ke yin amfani da yanayin da ake ciki domin tsauwalawa al’umma wanda kuma hakan bashi da amfani ko kadan.
Sai kwamishinan ya yi amfani da wannan damar inda ya yi kira ga Malaman da su fadakar da yan kasuwar su daina tsauwala farashin kayan da suke Sayarwa, saboda yin hakan bai dace ba ko kadan.
Ishaq Shehu Dabai ya kuma ba Malaman tabbacin cewa za a yi aiki tare domin ci gaban Jihar Katsina da kasa baki daya.

Kasancewar Gwamnan Jihar Katsina Dokta Dikko Umar Radda ya san muhimmancin wannan al’amarin da ke shafar al’umma ya sa ya bayar da umarnin kiran wannan taron tun da farko ta yadda jama’a za su samu sauki.

” kuma yace mu tabbatar maku yanzu haka Gwamnatinsa tana ta tsare, tsare za ta sayo abinci ta rabama Al’umma domin rage masu radadi”, inji kwamishina Ishaq Dabai.

Kwamishinan ya kuma ba Malaman tabbacin cewa zai yi aiki dari bisa dari tare dasu, saboda haka yana bukatar hadin kai da goyon bayansu domin ci gaban harkokin addini a Jihar Katsina”.

Shima a nasa Jawabin na godiya mataimaki na musamman ga Gwamnan Katsina a kan harkokin addini Alhaji Sabo Musa Hassan,  godiva ya yi wa Malaman a kan yadda su ka amsa goron gayyatarsu, inda shima ya jaddada neman hadin kan Malaman da goyon baya domin ganin harkokin addini a Jihar Katsina sun ci gaba.

Taron dai ya samu halartar Babban sakataren ma’aikatar Malam Surajo Dalhat Abukur, Malaman Addini daga bangarori daban daban.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.