Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Musa Bawa FCNA, Kodinetan kungiyar APC ciki da waje ne a Jihar Kaduna, da suke yi fafutukar yada manufofin jam’iyyar da kuma tallar baki dayan yan takarar ta tun daga Sama har kasa.
“Muna yin murnar nasarar da mai girma Sanata Uba Sani, hadimin Jihar Kaduna ya samu a kotun kolin Najeriya inda aka tabbatar masa da nasarar lashe zaben Gwamnan Jihar ba tare da wata tantama ba.
Daga wannan shekarar har zuwa shekarar 2027 ya zarce har zuwa 2031 da izinin Allah, saboda ayyukan da yake yi na ci gaban al’umma ta ko’ina wanda hakan ya nuna ta kowane bangare akwai Gwamnati a Jihar Kaduna.
Alhaji Bawa FCNA, ya ci gaba da bayanin cewa nasarar da Gwamna Uba Sani da Gwamnatinsa hade da jam’iyyar APC suka samu nasarori ne guda biyu ga nasara a kotun daukaka kara da kuma ta kotun koli a yau Juma’a sannan ma ga nasara a zabe na gaskiya da gaskiya har Uba Sani ya tabbata cewa zabin al’ummar Jihar Kaduna ne.
Bawa FCNA, “kungiyar APC ciki da waje ta zagaya kananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna tun da akwai wakilai a ko’ina a dukkan wannan kananan hukumomin baki daya, wanda hakan ne yasa ko a lokacin da za a zabi kungiyoyin da za su wakilci Gwannati har da APC ciki da waje aka zaba domin manyan kungiyoyi su gudanar da aiki. Kuma an tura wannan kungiya ta ciki da waje karamar hukumar Giwa domin aiwatar da aiki kuma mun yi aiki tukuru wajen neman jama’a har APC ta samu nasarar lashe zaben Gwamna da na yan majalisu biyu”.
FCNA ya kara da jaddada cewa Gwamnatin da Sanata Uba Sani ke yi wa jagoranci za ta ci gaba da ayyukan ciyar da kasa da al’ummarta gaba kamar yadda aka Sani wanda a halin yanzu har an fito da tsarin biyawa yara kudin makaranta an kuma rage kudin da dalibai ke biya na makaranta, an kuma tura wadansu dalibai yan Jihar Kaduna makarantu a kasashen waje suna karatu, an gyara ma’aikatar kula da asibitoci an gyara ma’aikatar lafiya sannan kuma an tura Magunguna asibitoci ana kuma ci gaba da yin gyaran hanyoyi a Jihar Kaduna kasuwanni sun bunkasa ga kuma irin yadda tattalin arzikin kasa ya dawo a Jihar Kaduna, wanda sakamakon hakan ne duk wanda ka gani murna yake yi a Jihar”.
“Muna yin amfani da wannan damar mu yi kira kamar yadda mai girma Gwamnan Jihar Kaduna ya fadi wato yin kira azo a gina Jihar Kaduna baki daya , saboda haka duk mai kishin Jihar Kaduna yakamata yazo a ta fi tare, kamar yadda aka taru a nan ake yi wa Gwamnan Jihar Kaduna murnar samun nasara a kotun koli. Kasancewar Gwamnatin Sanata Uba Sani Gwamnati ce ta kowa da kowa duk a ta fi tare, ko mutum na Kudanci, tsakiya ko yankin arewacin Jihar Kaduna duk nasa ne ba wani bambanci ko daya hakan ya sa duk aikace aikacen da ake yi ana yi ne a kowane yanki guda uku baki daya.
Musa Bawa FCNA, ya kuma yi kira ga mabiya al’ummar Jihar Kaduna da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwannati domin wannan Gwamnatin ta Sanata Uba Sani hakika akwai alkairi a tare da ita kuma alkairi zai samu kowa da yardar Allah”.