Home / Big News / TARON APC A ZAMFARA: Gwamna Lawal Ya Tabbatar Da Cewa Ƙarfin Gwamnati Na Rataye Ne Da Kyawawan Tsare-tsaren Jam’iyya

TARON APC A ZAMFARA: Gwamna Lawal Ya Tabbatar Da Cewa Ƙarfin Gwamnati Na Rataye Ne Da Kyawawan Tsare-tsaren Jam’iyya

 

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa nasara da ɗorewar kowace gwamnati na da alaƙa kai tsaye da ƙarfinta a fagen siyasa, musamman yadda jam’iyyarta ke da tsari mai ƙarfi da haɗin kai.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da ya halarci taron zaɓen shugabannin jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, wanda aka gudanar a filin baje kolin kasuwanci da ke Gusau.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, wakilai 745 daga ƙananan hukumomi 14 da kuma mazabu 147 na jihar ne suka zaɓi sabbin shugabannin jam’iyyar APC ta jihar ta hanyar amincewa da juna ba tare da gardama ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Sabuwa Balarabe, wadda ta jagoranci kwamitin gudanar da zaɓen, ita ce ta tabbatar da sakamakon tare da halartar rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar.

A jawabin da ya gabatar, Gwamna Lawal ya bayyana taron a matsayin lokaci mai muhimmanci kuma mai ma’ana ga ci gaban jam’iyyar, yana mai cewa hakan wata dama ce ta ƙarfafa tsarin jam’iyya da inganta dimokuraɗiyya a cikinta.

Ya ce, “Wannan tsari da ya kai ga zaɓe, tabbatarwa da kuma rantsar da sabbin shugabanni, wani muhimmin mataki ne da ke ƙara tabbatar da gaskiya, adalci da sahihancin jam’iyyarmu a matakin jiha da ƙasa.”

Gwamnan ya kuma gode wa shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa bisa jagoranci da goyon bayan da suke bayarwa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya a cikin APC, tare da yabawa kwamitin zaɓen bisa ƙwarewa da gaskiyar da suka nuna wajen gudanar da aikin.

Ya ƙara da cewa, taron ya kasance wata hanya ce ta sabunta alƙawarin jam’iyyar na haɗin kai, ladabi, haɗa kowa da kowa da kuma yi wa jama’a hidima, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da tsare-tsare da suka shafi tsaro, noma, ilimi, lafiya, gine-gine da bunƙasar tattalin arziki domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a Zamfara.

“Mun san cewa ƙarfan gwamnati yana fitowa ne daga ƙarfan ginshiƙin siyasa. Jam’iyya mai haɗin kai da tsari mai kyau ita ce ke samar da ingantaccen shugabanci da ci gaba. Wannan taro na da matuƙar muhimmanci wajen daidaita tsarin jam’iyya da manufofin gwamnati,” inji shi.

A nasa jawabin karɓar muƙami, sabon Shugaban APC na Jihar Zamfara, Honorabul Kabiru Moyi B/Magaji, ya yi alƙawarin inganta dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyar tare da ƙarfafa haɗin kai a tsakanin mambobinta.

About andiya

Check Also

Kaka Ya Ƙaddamar Da Takararsa A Kaduna Ta Arewa

  Daga Imrana Abdullahi A kokarinsa na ganin ya ci gaba da tallafawa dimbin al’umma …

Leave a Reply

Your email address will not be published.