Home / Big News / Shettima Yerima Ya Janye Takararsa

Shettima Yerima Ya Janye Takararsa

Shettima Yerima Ya Janye Takararsa

Daga Imrana Abdullahi
A cikin wani yanayi mai ban al’ajabi cike da alhini dab takarar kujerar majalisar dattawan Najeriya karkashin jam’iyyar APC a Mazabar Kaduna ta tsakiya Ambasada Kwamared Shettima Usman Yerima ya bayyana cewa ya janye takararsa domin jam’iyya, Bola Tinubu,Gwamna Sanata Uba Sani su samu nasarar da ya dace ta yadda kasa za ta ci gaba.
Ambasada Shettima Usman Yerima ya bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da ya kira da aka yi a Otal din Kwamand da ke cikin garin Kaduna.
“Na janye takara ta ne ba domin an matsa Mani ba, ko an tilasta Mani ba, na janye ne domin kashin kaina da nufin bayar da dama jam’iyya da Gwamna Uba Sani da kuma shugaban kasa Bola Tinubu su ci gaba”, Inji Shettima Yerima.
Kwamared Shettima Yerima ya kuma yi godiya ga xaukacin kungiyoyi tun daga kan Kafasiti da dukkan kungiyoyin da ake tafiyar Nan tare da su tun lokacin da ya fara yin takarar neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar dan majalisar dattawa domin ya wakilci Mazabar Kaduna ta tsakiya, duk muna godiya ga kowa a bisa gudunmawar da ya bayar wajen wannan tafiyar.
Ya kuma yi wa kowa alkawarin cewa zai yi kokarin bayar da dukkan gudunmawar da ya dace kamar yadda aka sani domin ciyar da kasa tare da al’ummar ta  Gaba.

About andiya

Check Also

Time to End Motion Without Movement in Nigeria’s Security Sector

By Sanusi A. S. Maikudi, FNIM Network for Justice, Kaduna The recent appointment of Major …

Leave a Reply

Your email address will not be published.