Home / Kasuwanci / Mun Kirkiri Ganyen Shayi Domin Bunkasa Nijeriya – Umar Kwanar Mai shayi

Mun Kirkiri Ganyen Shayi Domin Bunkasa Nijeriya – Umar Kwanar Mai shayi

Malam Umar Hashim Kwanar Mai shayi, masani ne a kan ilimin tsirai da yayan itatuwa kuma masani a kan cututtukan jikin dan Adam daban daban da ya yi bincike na tsawon sama da shekaru 35 inda ya gano cututtuka da kuma magungunansu ta hanyar yin amfani da yayan itatuwa da tsirai, sakamakon yin wannan bincike ya kuma samu gano hangen shayi kala kala inda ya kirkiro kala Goma (10) a halin yanzu da jama’a suke mamakin wannan kokarin kasancewa a da can sai daga kasashen waje kawai ake samun irin wannan ganyen shayin, ya kuma yi wa wakilinmu Mustapha Imrana Abdullahi karin bayani kamar haka ayi karatu lafiya.
GARKUWA :Shin Malam yaya aka yi wannan batun ganyen shayin ya samo asali?
Malam Umar : To, Alhamdulillahi dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki,hakika wannan tambayar da ka yi wani abu ne da ba biyayye ba domin mutane masu sauraren rediyo da masu bibiyar dandalin Sada zumunta na zamani da kuma abin da ya shafi jaridu musamman irin yadda kukan bukace mu domin mu yi fashin baki a kan al’amuran da jama’a za su amfana a game da abubuwan rayuwa da kuma abin da ya shafi lafiyar jikin dan Adam.
Hakika wannan aiki ne da ya shafi shekaru sama da  35 ko kuma fiye da hakan bisa bincike a kan tsirai daban daban na kan fita daji domin in duba ita ce har ta kai ga ban iya fita saboda jama’a sun yi yawa sai dai azo min da kowane nau’i na itace na kan karanta shi kuma in jaraba shi kafin in Sanya shi cikin magani, Alhamdulillahi sana’ace wacce take daban daban saboda ina fitar da Magunguna na ruwa da abin da ya shafi Magunguna na Gari sannan ba zamu baka magani ba sai mun yi maka tambayoyi bisa irin cutar da ke daminka wanda hakan ya sa da wahala mu bayar da magani ba a samu abin da ake bukata ba.
Ba mun ce muna yi ba dari bisa dari amma muna kokari ta hanyoyi daban daban kusan duk abin da muke bayarwa abu ne da ake Cinsa domin daman a cikin abinci ne magani yake idan abu ya gagara ta bangaren abinci mukan tsallaka ta bangaren itacen da Allah ya halitta domin  Dabbobi su ci su rayu duk a cikin irin wannan itacen mukan yo kokari mu fitar da abin da zai yi amfani ga jikin dan Adam.
Kuma duk abin da zai zama illa ga dan Adam za mu yi kokarin kaurace masa bisa ga ka’ida ta Amana domin duk lokacin da ka shiga Amana ta jikin dan Adam dole ka tausayi, kada ka bayar da maganin da zai jawo hadari shi yasa a doka irin ta Magunguna idan ka yi kisa to, nauyi na kanka don haka duk maganin da zamu bayar sai mun tabbatar da ingancinsa kafin mu bayar da shi.
Kamar yadda Turawa sukan Gwada ga Dabbobi kusan mu muna lura da wane irin itace ne dabba take ci mafi yawa ita kanta Dabba akwai itacen da bata ci amma idan ta kamu da rashin lafiya sai ta ci wannan itacen domin ta samu waraka, wanann shi ne daga cikin hukima ta bayar da magani sannan hatta da zuma wane irin Ganye yake ci
Ganye ko fulawa yake ci ko ba mu hada da zuma ba zamu yi amfani da wannan Fulawa domin mun san shi wannan zuma da yaje ya ci fulawa har ya fitar da zuma a jikinsa ya tabbatar da akwai waraka.
Haka nan abin da ya shafi magani mai karfi mukan lura abin da ya shafi na iskoki sai mu lura wane itace ne Rakumi ya fi amfani da shi, duk abin da Rakumi ya fi amfani da shi mukan kamanta shi da abin da ya shafi larura irin ta Isaka sai mu yi kokari mu hada kuma da ikon Allah na za a samu matsala ba.
Sannan duk wadansu abubuwa da ya shafi na ganyayyaki muna lura da shi.
Hakika abin da ya shafi ganyen shayi daban daban mun fito da ganyen shayi kamar kala Goma kuma kowannensu idan muka ce maka na kaza ne to, idan da zaka hada shi ka sha hakika zaka ga amfaninsa kuma zai baka dandanon abin da muka ce, misali idan muka ce maka wanann na minti ne wato Na’a Na’a to in ka sha zaka samu na Na’a Na’a ne in kuma muka ce wannan na citta ne in ka sha shi zaka samu kamshin citta, idan muka ce wannan na Kanumfari ne idan ka sha shi zaka samu Kanshin Kanumfari, idan muka ce wannan kamshin Goriba ne idan ka sha shi zaka samu kamshin Goriba yake, in kuma muka ce wannan ya yi dai dai da Abarba to hakika zai baka kamshi ne na Abarba, haka mai kamshin Ayaba, in kuma na ganyen Doddoya ne da ake yin Kori da shi duk kamshin da dandano na  Kori zai baka
Saboda haka mun yi shi dala daban daban Karaci kamar yadda na gaya maka mun ce mun yi su kala Takwas muna son yin kala kala har Ashirin kusan duk abin da ake yin wannan ganyen shayi a Nijeriya ake da su, da akwai wanda ma idan ka gan shi sai ka ce daga kasar waje ake yinsa.
Saboda me Allah ya taimake mu da kasa mai kyau duk abin da aka shika ya kan fita da kyau ya kan kuma bayar da abin da ake bukata da kyau, saboda haka muka lura da cewa daga cikin wadannan ganyen shayin na waje akwai wanda mai Ulsa ba zai sha ba, amma mu na mu zai iya sha ba wata damuwa, wanda ke fama da fargaba ba zaka iya sha ba amma mu namu duk mai fargaba a hadin da muka yi masa mutum zai iya sha domin mun hada shi da abin da ya shafi sanyi na majina da abin da ya shafi sanyi mai shiga cikin jiki da kuma sanyin da ke shiga cikin jini da duk abin da ya shafi kansa da suke bata kafafe masu fa’ida a cikin jikin dan Adam irin majina, jinin da bargo duk mun hada wanann ganyen shayin wanda idan kasha zai baka fa’idar da baka ta ba tunaninta ba
Ka dai sha shayi amma zai baka fa’idar da baka taba tunaninta ba.
Muna kuma da wanda ke rage kitse duk mun hada shi hatta da wanda ke rage tumbi duk mun hada shi da wanda kesa cin abinci hatta wanda mata idan suna da Juna biyu idan suna yawan Amai to mun hada masu wanda za su sha idan am dafashi ya hana Amai din duk muna da wanda ke wanke Koda muna kuma da mai wanke kwakwalwa mun hada su kamar dai yadda na gaya maka shi ne mukan ambaci sunan itace guda daya, amma kayan da muka Sanya ba na itace guda daya ba ne kuma dukkansu suna dauke da abin da duk abinci ne saboda haka da zaka ce a tattar maka su kana iya hada su ka yi miya kana iya hada su ka yi Yaji kana iya hada su ka yi Kori duk wadannan ganyayyakin da muka hada muka yi ganyen shayin nan ba su da hadari a cikin dan Adam.
Domin ba su dauke da Nukotin ba su dauke da Kafen abin da suke dauke da shi abu ne mai dauke da Fasforin da kuma ma’adinai irin  mangaziyum da Bitamin C da G da D duka yana a cikin wannan ganyen shayi kuma haka zamu ci gaba da yinsa da ikon Allah.
GARKUWA : Wannan ainihin nau’i na Bitamin akwai wata na’ura ta Gwada shi ne ko ko dai cikin ilimin ne da Allah ya bayar aka samu irinsa?
Umar Kwanar Mai Shayi : wato kamar yadda na gaya maka kowane magani ba za mu amince mu hada shi ba sai mun Gwada, wani lokaci ma muna Gwadawa mu da kawunanmu da kanmu, mai makon mu ce sai an Gwada to tuni aka Gwada da kawunanmu kuma Bama tunanin tun da har mun Gwada da kanmu ba zai zamar mana hadari ba.
To sannan bisa ga ainihin bitaminat da yake dauke da shi nau’i daban daban ne dukkansu kowanne muna Gwada shi sannan mu duba me yake dauke da shi? domin muna amfani da yanayin kasar shi da aka hako shi da kuma yanayin da yake ciki domin akwai nau’i daban daban na sinadaran da na lissafa a can baya.
Domin duk wanda muka fitar da zamu fara amfani da shi ba a ranar sai mun bashi wata biyu muna dafawa a cikin shayin da muke amfani da shi saboda haka akwai bambanci ba zamu fitar da abin da zai zamo cuta ba saboda me likitanci Amana ne idan mutum bai rike amanar ba to Allah yana iya jarabar shiNa gaya maka mun fari wannan sana’ar a kalla shekaru 35 ko 36 da suka gabata muna aiwatar da haka amma wadannan ganyayyakin duka ba su dade ba da muka fara yi ta hanyar abinci kafin mu sarrafa su, su koma ganyen shayi kamar yadda ka gani kuma shi wannan ganyen shayin yadda ka san ana shigo da shi daga kasashen waje haka muka yi shi yadda ake zuba shi a cikin mazabin kasashen waje haka aka yi shi da inganci kwarai. Fatar my dai kasarmu ta zamo ta na iya yin komai ta sarrafa komai da hikimarta da basirarta illa fatan kawai shugabanni su shiga cikin abin domin ya bunkasa fiye da yadda ake tsammani.
GARKUWA : Ya zuwa yanzu akwai wani abu da kuke amfana daga Gwamnati ko wani bangarori na ta da masana’antu ko kirkirar wadansu abubuwa za a rika cewa ana bayar da tallafi?
Umar Kwanar Mai Shayi:  Ai na gaya maka irin dadewa da kuma yadda muka sa himma a kan lamarin har yanzu Gwannati bata shigo ba na ta ba mu wani tallafi babban dai abin da muke yi kusan yanzu bisa ga yadda ka’idojin Gwannati suke da duk hukumomi sai da muka je muka same su sai da muka nemi izini sannan aka ba mu kuma akwai kudin da muke dauka muna ba su, amma su har yanzu ba su kawo mana wani tallafi ba abin da dai muke fata shi ne muna yi ne domin kishin kasa saboda haka duk ba za su samu zama da karfi ba sai yan Nijeriya sun go yi bayan abin tukuna mutane su Sani abin da mu muke yi da kanmu ya fi inganci.
Amma idan yan Nijeriya ba su ba mu gudinmawa ba duk yadda muka so fitowa da wani abu zaka ga babu tasiri, saboda abubuwan da suka shafi cututtuka akwai itatuwansu kuma ga shi Allah ya bayar da ilimin abin, sannan idan shi wancan za a sha a dauki lokaci a warke to wannan cikin lokaci sai kaga da an sha sai a warke.
Kamar yadda na gaya maka itatuwa ne Allah ne ya fitar da su kuma a ka’idar magani wato baka fita wata kasa domin neman magana Alhali ga inda Allah ya halicce ka, mafi yawa wasu ma sai an fita da su kasashen waje kuma a dawo mana da su nan mu yi amfani da ganyayyakin da Allah ya tsirar da su nan a samu waraka.
Wasu ma da yawa shawara kawai muke ba su a kan abinci abin da ya shafi Dawa da Alkama kuma duk wanda ya yi amfani da su sai kaga ya zo yana godiya, ga ba ki daya suna ta cin abinci amma suna rama amma da muka ce masu abin da za su ci kada a cure dussa a cikin abin da za a sarrafa ayi abincin sai ga shi an samu lafiya wallahi duk sun zo sun yi godiya domin hatta da abin da ya shafi Tarugu,Albasa da Barkono, wasu sai su zo su gaya mana gabobinsu sun rike ga abincin da zaku yi amfani da shi wasu su ce majinarsu ta bushe sai muce ku yi amfani da kubewa idan kuna da ita domin duk wani abin da zai taimakawa gangar jikin dan Adam akwai su da yawa a cikin wannan kasa. Zamu iya dogara da wadansu abubuwan da ba sai mun sha kwayar magani ba, abincin mu kawai shi yasa muka bude wani shiri aboncinmu maganinku a gidanku muna yinsa a kafar gidan rediyo akwai wanda muka ce abincinku maganinku duk akwai shirye shirye irin wadannan kuma hatta da abin da ya shafi kafar yada labarai ta yanar Gizo da dandalin Sada zumunta duk muna yi ba tare da neman wani abu ba saboda mu kanmu Allah ne ya ba mu baiwar don haka ba zamu boye ba ko kadan.
GARKUWA: Muna godiya.
Umar Kwanar Mai shayi: Nima na gode kwarai.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.