Home / Labarai / Yan bindiga Sun Bindige Direban Sarkin Birnin Gwari Mai Suna Nasiru

Yan bindiga Sun Bindige Direban Sarkin Birnin Gwari Mai Suna Nasiru

Yan bindiga Sun Bindige Direban Sarkin Birnin Gwari Mai Suna Nasiru
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Kaduna na cewa yan bindiga sun halaka daya daga cikin Direban Sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Jibril mai Gwari na biyu, mai suna Nasiru.
Bayanan da muke samu daga wani daga cikin mataimakan mai martaba Sarkin na Birnin Gwari na cewa wannan Direban mai suna Nasiru ya gamu da ajalinsa ne da Yammacin yau Asabar a kan hanyarsa ta komawa Birnin Gwarin, sai yan bindigar suka budewa motar da yake tukawa wuta, motar dai irin wadda ke yi wa mai martaba jagora ce ko kuma rakiya mai suna ( Pilot)
A lokacin rubuta wannan labarin ana can ana kokarin yi wa marigayi Nasiru jana’iza.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.