GAMAYYAR hadin gwiwar shugabannin Jam’iyyar APC na Kananan Hukumomin shiyyar Kaduna ta Tsakiya sun yi kira da a sami wani kwakkwaran matsayi na girmamawa a ba tsohon Shugaban riko na Kaduna ta Arewa Honarabul Usman Ibrahim, wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa saboda biyayyarsa ga jam’iyyar.
Shugannin sun yi wannan kiran ne yayin wata ziyarar Sallah da suka kaiwa Honarabul Usman Ibrahim a gidansa na Abuja don nuna girmamawa gare shi a matsayinsa na mai ruwa da tsaki a Jam’iyyar ta APC wanda suka bayyana a matsayin wani ginshikin da ke nuna goyon baya da kishin kasa da suka lura ya yi amfani da dimbin kayan aiki da halaye masu kyau wajen ginawa da karfafa jam’iyyar a shiyyar.
Shiyyar yankin Kaduna ta Tsakiya ta kasance mafi yawan mutane daga shiyyoyi uku na Sanatoci a jihar tare da Kananan Hukumomi bakwai wanda suka hada da Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, Kajuru, Birnin – Gwari, Giwa, Igabi da kuma karamar hukumar Chikun.
Shugabannin wadanda suka isar da sakonninsu daya bayan daya, sun bukaci Sardaunan Badarawa da ya ci gaba da kyakkyawan ayyukan da yake yi wa jam’iyyar, inda suka kara da cewa aikin bayar da kyauta kana da aikin sadaukar da kai da kuma karamci wani abu ne mai muhimmanci a duniya.
Sun bayyana wasu gudummawar da tsohon shugaban karamar hukumar ya bayar wanda suka hada da saka fitilun kan titi masu amfani da hasken rana a wasu yankuna daban-daban na shiyyar, da suka hada da makabartar musulmai da kirista, karfafawa matasa da mata, tallafin karatu ga masu karamin karfi, ciyar da masu karamin karfi a lokacin azumin watan Ramadana da ya gabata a fadin shiyyar na Kaduna ta tsakiya da wasu sauran wurare.
“Sardaunan Badarawa ya banbanta kansa da irin ayyukan ci gaban mutane da dama da yake yi don taimakawa gajiyayyu da kuma hada kan membobi daban-daban na al’umma don cimma wata manufa daya.”
“Basirarsa ta bi da mutane ta hanyar dai-daita sahunsu ta kasance ba tare da nuna bambancin kabila, addini ko siyasa ba don haka wani abun alfahari ne.”
“Irin wadannan mutumen da ake yabawa a cikin al’umma, ya cancanci ya taka muhimmiyar rawa a jam’iyyarmu don ci gaba, hadin kai da ci gaban APC gaba daya a matakin jihohi da tarayya.”
“Babban hidimarsa ga jam’iyyar da kuma rayuwar yan adam ba za a iya lissafasu cikin sauki a shafukan jaridu ba, haka kuma kyawawan ayyukansa ba za su iya zama wani abun da za a mance dasu a cikin kannanin lokaci ba.”
“Duk da cewa ya rasa tikitin jam’iyyar ga Sanata Uba Sani a 2019 ta hanyar zama wanda ya zo na biyu, bai yi watsi da APC kamar yadda wasu su kayi ba amma ya ci gaba da kokarin gina jam’iyyarsa don tabbatar da ci gaba da nasarar babbar jam’iyyarmu.”
“A yanzu ya kamata a karrama shi tare da ba shi wata muhimmiyar rawar da zai rika takawa don ya kara fadada ayyukansa na sadaukar da kai “Inji su
Da yake mayar da martani bisa ga sakon shugabannin, Sardaunan Badarawa ya sake bayar da tabbacin gudummawarsa na ganin ci gabansu baki daya, tare da bayyana goyon bayansa da kwarin gwiwar a kan irin namijin kokari da karfin jagorancin gwamna El-Rufai don ganin ya kammala ayyukan ci gaban jihar da yake yi a halin yanzu.