Related Articles
Mustapha Imrana Andullahi
Babbar kotun da ke shari’ar Malam Inrahim Zakzaky da matarsa Zeenatu ta sake su bisa hujjar cewa hujjojin sha biyar da Gwamnatin Jihar ta bayar a gaban kotun ba su inganta ba.
Lauya Sadau Garba ne ya tabbatarwa manema labarai hakan a lokacin da aka kammala yanke hukuncin a kotun da ke Kaduna.
A sakamakon hakan kotun ta sake su, kuma bayanan da muke samu a halin yanzu sun tabbatar da cewa dukkansu baki daya sun dunguma zuwa garin Zariya da ke karamar hukumar Zariya cikin Jihar Kaduna a arewacin Najeriya
Za mu ci gaba da kawo maku irin yadda lamarin ya kasance.