Home / KUNGIYOYI / Za A Koyawa Matasa 500 Sana’o’in Fasahar Zamani

Za A Koyawa Matasa 500 Sana’o’in Fasahar Zamani

Mustapha Imrana Abdullahi
Cibiyar da ke kokarin ganin rayuwar matasa ta inganta mai suna IRIBID da ta kasance mai zaman kanta ta bayyana cewa ta shirya horar da matasa 500 sana’o’in da ake horar da jama’a ta hanyar amfani da yanar Gizo da nufin kowa ya samu damar dogaro da kansa.
Cibiyar ta bayyana hakan ne a wajen wani babban taron da majalisar dinkin duniya ta ware a shekarar 2021 domin matasa.
Shugaban cibiyar mai zaman kanta Malam Usman Machika ya ce horaswar za a yi ta ne tare da hadin Gwiwar kamfanin na’ura mai kwakwalwa na “Microsoft” reshensa da ke Najeriya.
Machika ya ci gaba da bayanin cewa za a karantar da matasan ne a fannonin ilimi guda Tara su samu damar dogaro da kawunansu.
Da suka hada da  “digital literacy, problem solving, global citizenship (networking) and youth interprenuership”.
Sauran kuma su ne  “curiosity and love for learning, communication skills, adaptability and conductive flexibility, accessing, assessing and analyzing information, self knowledge and emotional intelligence”.
Ya kara da cewa za a yi horaswar ne ta hanyar kasa daliban daki daki wato za a rarraba su daga wadannan sun kammala da safe wasu kuma su ci gaba daga inda wadancan suka tsaya duk da nufin karfafawa matasa Gwiwar samun ilimi mai inganci da zai amfani rayuwarsu duniya da lahira baki daya.
 Machika ya ce cibiyar tuni har ta fara aiwatar da horaswar a kan ilimin Fasahar na’ura mai kwakwalwa kuma za a yi shi ne tsawon kwanaki Bakwai a fannin bangarori biyar.
Ya ce Kuma kamfanoni kwamfuta na microsoft ne zai shirya jarabawar da daliban za su yi kuma kamfanin Microsoft din ne zai bayar da takardar shaidar kammala karatun ga dalibai.
Kamar yadda Machika ya bayyana cewa cibiyar na kokarin fadada horaswar ga ma’aikatan Gwamnati da wadanda suka ajiye aiki domin su amfana.
Tun da farko tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Shehu Abdullahi, yabawa cibiyar ya yi game da kokarin samar wa matasan da wannan horaswa.
Farfesa Abdullahi ya kuma shawarci wadanda za su yi karatun da su mayar da hankalinsu inda ya jaddadawa matasan cewa ta wannan hanya ce za su samu damar taimakawa kawunansu.
Abdullahi sai ya yi kira ga Gwamnati da masu ruwa da tsaki da su kawo kudin da za a samu sukunin aiwatar da wannan aikin ciyar da kasa gaba, musamman ganin cewa matasa ne da suka kasance manyan gobe ne za su amfana.
Da yake tofa albarkacin bakinsa jagoran kungiyar matasan Najeriya reshen Zariya Usman Mazadu, cewa ya yi alkalumman tattalin arzikin duniya ya nuna cewa kashi 54 na ma’aikata na bukatar samun horaswa nan da shekarar 2022.
Ya ce ma’aikatu a duk fadin duniya sun amince da batun samun horaswa ta yanar Gizo domin a samu sukunin aiwatar da harkokin kasuwanci da kuma samar da aikin yi ta hanyar zamani.

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.