Home / KUNGIYOYI / Mutanen Yankin Arewacin Najeriya Ba Na Sayarwa Ba Ne – Dokta Hakeem Baba Ahmed

Mutanen Yankin Arewacin Najeriya Ba Na Sayarwa Ba Ne – Dokta Hakeem Baba Ahmed

Mustapha Imrana Abdullahi
Al’ummar yankin arewacin Najeriya sun bayyana ra’ayinsu game da batun zaben shekarar 2023 mai zuwa, inda suka fara cewa duk masu tunanin za su iya sayen kuri’ar mutanen yankin su na ba ta wa kansu lokaci ne domin yankin ba na Sayarwa ba ne.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mai magana da yawun kungiyar Dattawan arewacin Najeriya Dokta Hakeem Baba Ahmed ya fadi hakan a wajen wani babban taron lacca domin tunawa da marigayi Dokta Yusuf Mai tama Sule dan masanin Kano da aka yi a dakin taro na kwalejin  bunkasa dabarun Noma da ke jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
A wajen taron laccar da gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu suka shirya karkashin jagorancin Kwamared Nastura Ashiru Shereef, taron ya samu halartar jama’a daga dukkan Jihohin arewacin Najeriya da suka hada da musulmi da Kirista tare da dimbin mahalarta a bangaren dalibai ta hanyar kungiyar daliban Najeriya.
“Muna kira ga daukacin al’ummar arewacin Najeriya da kowa ya bude idanunsa domin tantancewa a lokacin zaben 2023 ta yadda za su zabi shugaban da zai taimaki rayuwa da inganta harkokin kasar baki daya.
Dokta Hakeem Baba Ahmed, ya kuma yi magana da kyakkyawar murya game da mutanen da ke tunanin cewa su na da wadatar da za su iya biyan kudi domin su sa yi kuri’a ko yancin mutanen arewacin Najeriya su Sani cewa mutane da yankin Arewa ba na Sayarwa ba ne saboda haka ya dace masu tunani sabanin hakan su san me suke yi don canza tunani game da yankin Arewa.
Hakazalika game da masu yin kururuwar a ware wai in har ba su samu shugabancin Najeriya ba a 2023, Dokta Haleem Baba Ahmed ya ce ai sai dai Allah ya raka Taki Gona kawai amma haka kawai ba wanda zai dauki mulki ya mika wa wadansu mutane ba tare da tantance tsare tsaren Dimokuradiyya ba
Sai ya yi kira ga matasan Arewa da Najeriya baki daya da su Sani fa makomar kasa da kuma Yankewa kowa hukunci game da lamarin zabe na hannunsu saboda haka kada su rika tunanin wani ko wasu gungun mutane ne zai taimaka masu haka kawai.
Da yake gabatar da kasida a wajen taron laccar tunawa da marigayi dan masanin Kano Alhaji Dokta Mai tama Sule Dan masanin Kano, domin zaburar da matasa manyan gobe domin samun kyakkyawa ingantacciyar akida da za ta zama abin ko yi ga al’umma Dokta Riya’uddeen Zubairu Mai tama, wanda Malamin jami’a ne a kasar Indiya cewa ya yi akwai bukatar matasa su tashi tsaye domin a samu gyaran da zai tabbatar domin mayar da bara Bana musamman idan aka yi la’akari da irin yadda tarbiyya da yan uwantaka ta kasance a halin yanzu.
“A zamanin da can kusan dukkan inda mutum ya samu kansa a arewacin Najeriya zai ga ana zaman tare ne cikin ladabi da girmama Juna ba tare da Juna wani bambanci ko akida ba”.
” ina muka Baro koyarwar magabata a Arewacin Najeriya lokacin da babu wani nuna bambanci ko kadan, sabanin yanzu da ake samun wani yanki na Arewa ake samun sukurkucewar Lamura da sai ka ga wani yanki ana samun bambancin addini, kabilanci ko a wani bangaren Arewa ake fama da batun yan bindiga, barayin Shanu ko mutane ana neman kudin fansa da sauran dimbin matsaloli da dama?
Saboda haka ana bukatar kowa musamman ma matasa su kara bude idanunsu domin samar da gyaran da zai ciyar da kasa gaba.
A na ta tsokacin wata yar fafutuka Hajiya Dokta Naja’atu kira ta yi ga matasa da su tashi tsaye wajen bayar da gudunmawarsu ta yadda za a samu wadanda za su ja ragamar kasa a nan gaba, domin kamar yadda ta ce su shekaru sun fara yi masu yawa don haka matasa ne ake saran su bayar da ta su gudunmawar kasa ta ci gaba.
“Wa kuke jira ya zo domin ya yi maku aikin ci gaban kasa? Ai mun bayar da gudunmawarmu don haka matasa kowa ya tashi tsaye, sai ta bayar da misalan irin yadda Marigayi Murtala, Obasanji da Buhari suka zama shugabanni a Najeriya lokacin su na da shekaru kalilan ba kamar yanzu ba da matasan da shekarunsa ba su da yawa amma kuma ba su ma ko samu damar shiga a dama da su ba a cikin harkokin Gwamnati balantana su saran zama wani abu”, inji Naja’atu.
Jama’a da dama dai sun gabatar da jawabai da ke nuni tare da yin kira ga matasa su yi ko yi da irin rayuwar marigayi Dokta Yusuf Mai tama Sule Dan masanin Kano.
Dimbin dalibai da suka hada da Maza da Mata da dama ne suka halarci taron laccar da aka yi wa matasa allurar fadakarwa kan su Sani su ne manyan Gobe.

About andiya

Check Also

Dangote cement export of clinker, cement increase by 87.2%

  Management of Dangote Cement Plc has revealed that the company dispatched seven ships of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.