Home / News / AN KADDAMAR DA MAGAJIN BALARABE MUSA A PRP

AN KADDAMAR DA MAGAJIN BALARABE MUSA A PRP

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
AN bayyana jam’iyyar PRP da cewa ita ce jam’iyyar da babu wani bangare a cikinta ko kadan
An bayyana hakan ne a wajen babban taron kaddamar da Magajin marigayi Alhaji Balarabe Musa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, wanda kuma ya Gaji marigayin shi ne Kassim Balarabe Musa, daya daga cikin yayan marigayin kuma taron ya samu halartar dimbin jama’a daga ciki da wajen Jihar Kaduna.
Kuma duk wanda ko wasu da suke cewa akwai bangare to sune bangaren, amma PRP a dinke take guda daya ce ba wani bangare ko kadan.
Shugaban jam’iyyar PRP na karamar hukumar Soba Alhaji Isa Soba,ya ce duk dan shekara Talatin ko Talatin da biyar bai san PRP ba sai dai a yanzu za a koya masu me ake nufi kuma meye PRP, sai dai yan shekaru 50 zuwa 60 dune suka san meye PRP.
Alhaji Isa Soba, “abin da aka fadi a game da halaye Malam gaskiya ne,PRP its ce kadai jam’iyya a Afrika ba wai a Nijeriya ba
Mu muka nemi a ba mu wani daga zuri’arsa ya zama Khalifa, ayi hakuri domin hakurin ya kawo har a yanzu muke tare da tafiyar nan har yanzu.
PRP bata da wata matsala sai dai shure kawai, a hada kai, muna fatan za a yi hakuri
Auwal Ibrahim daga Kano shugaban tabbatar da canji irin na gaskiya a kasa baki daya
“Duk wanda ya kasance dan PRP mai akida ta gaskiya domin son a samu canji dai dai yake da mutane miliyan daya”, inji Auwal.
“Ya kara da cewa muna nan a cikin hasken PRP har abada domin in mun mutu wasu ne za su ci gaba daga inda aka tsaya”.
“Katin jam’iyya ake Sayarwa a samar da Ofisoshi da sauran hidimar jam’iyya domin kowa ya zama da cikakke ba Bawa ba,a 1979 PRP ta sa an samu wakilcin kowa ne dan kasa a Najeriya, sai mun amince a cikin Rubin zuciyarmu cewa za mu iya kawo zaben Najeriya”.
Ya bayyana Malam Kassimu da cewa zai iya jawo nasarar da kowa ke bukata domin ya na da jajircewa da son PRP, domin a kan haka ne Malam Aminu Kano ya ce ya na ganin haske a can nesa to wannan haske zamu kai hare shi.
Honarabul Kassimu Balarabe Musa ya ce hakika wannan babban takalmin da aka ba ni ya fi karfi na amma duk inda aka ce an baka wani matsayi to ya dace ka daure ka rike domin alkairi ne.
“Hakika wannan matsayi su Soba ne suka ba ni sai fatan Allah ya ba ni ikon rikewa domin kasa da al’ummarta su amfana”.
Ayi hakuri ga zabe ya zo don haka a hada kai ayi tafiya daya shugabanni daya ba tare da samun Rabe Rabe ba.
Jama’a ayi hakuri abi Alhaji Falalu Bello wanda shi ne Malam Abdulkadir Balarabe Musa ya dauka a cikin mutum miliya ya bashi domin ya ga cancantarsa
“Kuma Falalu Bello shi ne sunansa yake a wurin INEC don haka ina kan Gwiwa a kasa
Kassimu ya kuma yi kira ga Malam Nasiru Ahmad El- rufa’i ya shigo cikin jam’iyyar PRP domin wannan jam’iyya ta PRP ita ce gidan aiki
Ya kuma yi godiya ga yayan jam’iyyar APC da suka zo taron PRP domin mu a ciki  PRP PRP Adam ya fi komai muhimmanci ko talaka ko me kudi
Ayi hakuri da abin da ke kasa azo a goyi bayan Alhaji Falalu Bello a matsayin shugaban PRP na kasa.
“Ina godiya ga mutane  da suka ba ni wannan jagoranci duk da ina ta kaucewa amma dai suka ce sai ni
Mista Mark ya ce a matsayinsu na shugabannin jam’iyya a Jihar Kaduna za su bayar da hadin kai da goyon baya.
Mataimaki Tom Mai Yashi, wanda ya samu wakilcin Mista Samuel Badoms, da ya gabatar da jawabi a wajen taron inda ya bayyana irin nagarta da irin yadda marigayin ya gabatar da rayuwarsa inda ya yi kira ga yayan jam’iyyar PRP da su yi hakuri a tafi tare domin duk kowace jam’iyya ana samun wannan don haka ayi hakuri, PRP daya ce gida daya ne kuma guda daya ce.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.