Home / News / AIKI JAWUR YA SAMU YAN SIYASA A NAJERIYA – ALIYU WAZIRI

AIKI JAWUR YA SAMU YAN SIYASA A NAJERIYA – ALIYU WAZIRI

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Wani fitaccen dan siyasa mai kokari wajen inganta rayuwar al’umma Kwamared Aliyu Muhammad Waziri Santurakin Tudun Wada Kaduna da ake yi wa lakabi da dan marayan Zaki, ya fito fili ya bayyana cewa akwai babban aikin da ya samu yan siyasa kuma aiki ne Ja Jawur a gabansu.
Kwamared Aliyu Muhammad Waziri ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin tattaunawa a kan al’amuran yau da kullum da suka shafi kasa ko duniya baki daya mai su na “Babban Gammo” na gidan rediyo da Talbijin na DITV da ke Kaduna arewacin tarayyar Najeriya.
Aliyu Waziri wanda shi ne shugaban kungiyar da ke koyawa matasa Noman zamani da ya kasance mai rike da sarautun gargajiya kala daban daban wanda al’ummar Najeriya suka bashi ya bayyana cewa idan aka yi tariyar abin da ya faru a shekarar 2015 lokacin da aka zabi shugaban kasan ba babu maganar jam’iyya domin ita maganar jam’iyya duk wani lamari ne na ra’ayi kawai
” saboda haka ya na da kyau a duba me al’umma suke ciki wanda du ba da hakan ne ya kai ga aka zabi shugaban da ke kan mulki a halin yanzu ba tare da la’akari da batun jam’iyya ba kawai dai mulki kawai ake son ya dawo Arewa ba wata magana”, inji dan marayan Zaki.
San turakin Tudun Wada ya ci gaba da bayanin cewa duk irin Tururuwar da aka yi lokacin zabe a 2015 shi ne mulki kawai ya dawo Arewa ba maganar wata jam’iyya mulkin dai ya dawo Arewa kawai.
“Saboda mulkin Najeriya na Arewa ne, amma saboda samun baragurbi ya sa mulkin ba a ga ne masa duk da ya dawo Arewa kuma dan Arewa ke yinsa”.
Ya kara da cewa ilimi, Zahiri da Siyasa duk wadansu abubuwa ne daban daban saboda haka muke kokari mutane su ga ne cewa akwai sauran shekarun da ya ragewa yan Arewa su kasance a mulki tun lokacin zamanin Obasanjo da ya kwashe shekaru Takwas sai Umar Musa matigayi ya yi shekaru biyu sannan Jonathan ya karba ya yi shekaru Shida a kan mulki sai yanzu Buhari duk da haka idan an kammala lissafi za a ga akwai sauran lokacin yan Arewa da ya rage su cikasa a mulkin Najeriya.
Idan hali ya yi zamu kawo maku ci gaban wannan doguwar tattaunawa da Aliyu Muhammad Waziri dan marayan Zaki ya yi.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.