Related Articles
Imrana Abdullahi
Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna Honarabul Isa Muhammad Ashiru Kudan, ya bayyana cewa tuni wani kwamitin masana karkashin wani Furofesa daga jami’ar Ahmadu Bello Zariya suka yi aikin fitar da kundin da za a yi aiki da shi da zarar ya kafa Gwamnati a Jihar Kaduna.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta bbc hausa a Kaduna.
Honarabul Isa Ashiru Kudan ya ce daga cikin wannan aikin fitar da kudirorin ne suka tace aka fitar da kudirori guda biyar da za a aiwatar a matsayin aikin da za a yi wa jama’ar Jihar Kaduna domin kasa baki daya ta amfana.
Isa Ashiru, ya ci gaba da bayanin kudirorin kamar haka inda ya ce akwai na farko shi ne samar da ingantaccen tsaro, samawa matasa Maza da Mata aikin yi musamman ta hanyar koya masu sana’o’in hannu da za su dogara da kawunansu har wasu su amfana da abin da suke yi, sai kuma Inganta harkar ilimi, Noma, za a tabbatar da koyawa dimbin matasan da suke a Jihar Kaduna yadda za su yi sana’a da ilimin da suka koya ga kuma tsarin yin Noman rani da na Damina.
Ya kuma tabbatar wa kafar yada labaran bbc hausa cewa akwai kyakkyawar dangantaka mai kyau tsakaninsu da wadanda suka yi takarar neman kujerar fitar da Gwani a jam’iyyar PDP kuma nan gaba kadan za su zauna da su domin fitar da yadda za a tafiyar da gangamin neman zabe a Jihar.
“Bayan an kammala zabe kowa sai da naje gidansa na kuma tattauna da shi don haka dangantakar mu mai kyau ce a tsakanin dukkan yan takarar da muka yi takarar neman zaben fitar da dan takarar Gwamna a jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna.
“Za kuma mu dawo da tsarin hakiman da Dagatai da suke a yankunan karkara domin su na da matukar amfani wajen samun ingantattun bayanan sirri a kan harkar tsaro, su ne fa suka fi kusa da jama’a don haka suna da labarin abin da jama’a suke ciki kuma meke faruwa a kowane lungu da sako da al’umma suke zaune”.