Home / Lafiya / A Kaduna Abin Jiya Zai Dawo Ne

A Kaduna Abin Jiya Zai Dawo Ne

Akwai Yuwuwar Saka Dokar Hana Fita A Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i, ta gargadi jama’a game da yuwuwar sake shiga dokar hana fita kashi na biyu madamar mutane ba su kiyaye da ka’idojin hana dauka da yada cutar Korona ba.
Bayanin gargadin na kunshe ne a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai a Kaduna da ta fito daga ma’aikatar lafiya karkashin jagoranci Dokta Amina Baloni.
Kamar yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana ta hannun kwamishiniyar lafiyar cewa kamar dai irin yadda lamarin ya faru a can kwanakin baya, inda Gwamnatin ta rika kula da yadda lamarin yaduwar cutar yake a wancan lokaci karo na farko da aka yi hanzarin daukar mataki domin dakile yaduwar cutar
Kwamishiniyar ta lissafa irin yadda lamarin ya fara a tun farko da yadda Gwamnatin ta dauki matakin gaggawa, a kan haka ne Gwamnatin ke gargadin jama’a da su ci gaba da daukar matakan kiyayewa a dukkan wuraren gudanar da rayuwa baki daya domin kaucewa daukar matakan gaggawa a karo na biyu da kamar yadda Gwamnatin ta bayyana cutar Korona na yaduwa a Jihar Kaduna.
” Alkaluman masu dauke da cutar Korona na kara yin sama, saboda haka ne Gwamnatin Jihar Kaduna ke shawartar jama’a su ci gaba da kiyayewa musamman bin dukkan ka’idojin da hukumar NCDC ta kasa da ke yaki da cutar suka bayyana”, inji kwamishina Amina Baloni.

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Kaddamar Da Manyan Ayyuka A Bakura Da Maradun

A ci gaba da gudanar da bukukuwan cika shekara ɗaya a karagar mulkin jihar Zamfara, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.