Home / Big News / Takin Zamanin Da Ake Saye Cikin Sauki A Jihar Kaduna Ba Na Gwamnati Bane – Bincike

Takin Zamanin Da Ake Saye Cikin Sauki A Jihar Kaduna Ba Na Gwamnati Bane – Bincike

Mustapha Imrana Abdullahi
Sakamakon irin korafe korafen da jama’a suke yi a kan yadda ake sayar da Takin zamanin da aka ajiye a cikin Dakin ajiyar kaya na Gwamnatin Jihar Kaduna suka yi kamari yasa wakilinmu zagayawa wuraren da ake sayar da Takin naira dubu biyar domin saukaka wa mutane.
A wadansu wuraren an kara saukakawa manoma ne ta hanyar cewa duk mai so ya bi layi da kudinsa domin a bashi buhuna biyar a kan kowane buhu mutum zai biya naira dubu biyar.
Hakan ta Sanya jama’a da dama yin tururuwa zuwa wurin da aka ajiye Takin zamanin domin su saya.
Amma sai dai korafi ya taso ne a wurare irin na wurin ajiyar Taki na unguwar Rigachikun sa ke karamar hukumar Igabi, inda har ta kai kamfanin da ya kawo Takin ya rufe wurin ajiyar Takin, sakamakon irin yadda wadansu mutane suka kekasa kasa cewa dole kawai a raba Takin a matakin Mazabu mazabun da suka hadu suka yi karamar hukumar ta Igabi.
A binciken da muka yi wakilinmu ya samo cikakkun bayanai da suke cewa Takin zamanin ba na Gwamnati bane, illa dai an yi yarjejeniya ne da Gwamnati da kuma kamfanonin da za su samar da Takin cikin sauki domin manoman Jihar Kaduna su samu rahusa.
A wasu Jihohin da suka hada da Jihar Kaduna idan mutum na son Takin zamani sai ya Sanya kudi naira dubu Bakwai zuwa sama kafin a samu sayen takin a kasuwa, amma saboda irin yarjejeniyar da Gwamnatin Jihar kaduna ta shiga da wasu kamfanoni na cewa Gwamnatin za ta bayar da wurin ajiye takin wato ( sito) ba tare da kamfanonin takin ko masu sayowa su sayar sun biya ko Sisi ba na ajiya.
Kuma binciken namu ta tabbatar mana da cewa an samu sauki kwarai madadin a sayi taki naira dubu biyar da dari biyar sai aka samu saukin naira Dari biyar a kan farashin Gwamnati idan kuma an zo saye a kasuwa hannun yan kasuwa a yanzu takin na kaiwa dubu Bakwai.
Wannan ce tasa wasu daga cikin yan siyasa da ma’aikatan karamar hukuma suke ganin kawai a kai Takin a mazabu domin kamar a karamar hukumar Igabi, wasu kansiloli na ganin cewa a kai Takin Unguwar Rigachikun kamar an watsar da manoman ne kefe daya domin sai sun yi tafiya mai nisa kafin su tarar da garin Rigachikun, sannan du Sanya kudinsu su sayi takin wanda kai shi zuwa garuruwansu a matsayinsu na manoma abin zai zamar masu da wahala.
Ga dai yadda aka fayyacewa wakilinmu yadda yarjejeniyar take wato Gwamnatin Jihar Kaduna za ta bayar da wurin ajiyar Takin sai kuma kamfanin Golden da aka shiga yarjejeniyar da shi zai samar da Takin zamanin kuma za a sayar da Takin ga manoma naira dubu biyar.
Saboda binciken ya tabbatar mana da cewa kamfanin Takin zamani na Golden zai ba abokan huldarsa duk buhu a kan naira dubu hudu da Dari biya. Sai su kuma abokan huldar da za su sayi Takin a hannun kamfanin su biya kudin motar Dauko shi zuwa wuraren ajiyar da Gwamnati ta bayar bayan sun biya kudin leburori na lodi da saukewa sai su sayar da shi naira budu biyar ( 5000) ha manoma a kowane buhu, kuma a wurin ajiyar Takin Tigachikun an yi ka’idar Sayarwa duk wanda ya shiga layi zai saya buhu biyar kawai za a sayar masa.
Amma a wurin rabon Takin na U guwar Tigachikun mun tarar da dimbin korafe korafe da suka hada da cewa wasu yan kasuwa sun rabawa mutane kudi ciki har da kananan yara kamar yadda muka gani a faifan bidiyo a lokacin da wakilinmu yana gudanar da bincikensa.
Saboda su yan kasuwan sun samu inda za su sayi Takin da arha su kuma su sayar da tsada a cikin kasuwa idan manoma sun zo sayen Takin da za su yi amfani da shi a Daminar Bana.
Saboda haka muka gano cewa Takin da ake Sayarwa manoma a Daminar Bana ba na Gwamnati bane kamar yadda wadansu yan siyasa suke korafi a kai tun farko wanda hakan tasa suke cewa a kai masu shi mazabunsu, sai dai Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I ta yi kokarin yin wannan shirin me domin manoma su samu saukin kudin Takin da a wasu wurare yake kaiwa dubu Bakwai, Takwas zuwa sama da hakan.
An samar wa jama’a sauki kwarai a wurin sayar da yakin na Rigachikun domin kuwa kamfanin Takin zamanin ya Sanya dokar cewa shi ba zai karbi kudi a hannu ba kuma kowane mutum ke bukatar Takin dole sai yaje Banki ya biya ta asusun ajiyar kamfanin da sunansa ba da sunan mai ajiyar kudin ba, wanda binciken mu ya nuna mana cewa zai yi wa mutanen karkara wahala kwarai ga shi kuma su ne manoman na gaskiya.
Sai aka tabbatar masu da sauki bayan an roki kamfanin Takin zamanin domin a samu amincewarsa, mutane su bi layi da kudin su a hannu na buhuna biyar biyar kuma a kan naira dubu biyar a kowane buhu don haka Takin zamanin da ake Sayarwa a Jihar Kaduna binciken mu ya gano cewa Bana Gwamnati bane, Takin kamfani ne, haza wasalam.
Za a iya samun wanda ra rubuta wannan mukalar a lambar waya kamar haka  a whatsapp 0809727 3335.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.