….INA FATAR GAMAWA LAFIYA
A kokarin mai takarar mataimakin shugaban kasa karkashin tutar jam’iyyar APC, Jirgin tuntuba da ganawa da jama’a na Alhaji Kashim Shatima ya Isa Jihar Kano domin ganawa da kuma tattaunawa da shugabannin al’umma, manyan yan kasuwa da dukkan masu ruwa da tsaki a game da batun zaben shekarar 2023 mai zuwa.
A lokacin da Kashim Shatima tare da Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje sun ziyarci babban hamshakin dan kasuwa Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda ya kasance jagoran al’umma ne a kasa baki daya, ya shaidawa mai takarar mataimakin shugaban kasar cewa a wannan lokacin da ya kai shekaru 91 bays ko jin dadin rayuwa kawai fatansa shi ne gamawa da duniya lafiya.
Dan shekaru 91 Dantata, ya samu damar yin tafiye tafiye zuwa dukkan Jihohin Najeriya ya kuma samu abokai da yawa tun a zamanin kuruciyarsa amma kuma da wahala ya iya nuna mutane 10 da suke a raye a halin yanzu.
” Ni kadai ne na rage a yanzu a cikin yan uwana da nake zaune da Jikoki”, inji Aminu Dantata.
Sai Dantata ya ce hakika yana rokon jama’a ga duk wanda ya bata mawa a cikin ya na sane ko da rashin Sani ya na bukata da yin kiran ya yafe masa saboda shi ya yafe wa kowa ga duk wanda ya bata masa.
Sai babban dan kasuwan ya bayyana cikakkiyar godiyarsa ga Kashim Shettima da ya kawo masa ziyara da kuma irin kokarin da ya yi na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.
“Muna fatar kada Allah ya bar my da iyakar mu kawai, muna yin addu’ar Allah ya ci gaba da taimaka mana mu kara bin hanya madaidaiviya ya kuma yi mana kariya”,.
Daga cikin mutanen da suke cikin tawagar sun hada da Musa Gwadabe, Janar Lawal Jafaru Isa da Tanko Yakasai.
Tawagar dan takarar kuma ta kai ziyara zuwa inda ake yin aikin cibiyar kula da cutar kansa da aka kusa kammala wa.