Home / Labarai / A Shirye Muke Muba Gidauniyar A A Charity Goyon Baya – Jihar Kebbi

A Shirye Muke Muba Gidauniyar A A Charity Goyon Baya – Jihar Kebbi

Daga Imrana Abdullahi
An bayyana ayyukan Gidauniyar Tallafawa marayu, gajiyayyu da masu bukata ta musamman ta A A Charity a matsayin abin da ya dace kowa ya hada Gwiwa da su domin neman lada duniya da lahira.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Umar Abubakar Arugungu ne ya ankarar da jama’a game da wannan bukatar a wajen babban taron kaddamar da sababbin Jagororin gidauniyar da kuma bayar da tallafin karatu ga marayu da mabukata Maza da mata da aka koyawa sana’o’i daban daban domin su kama sana’ar dogaro da kai.
Taron dai an yi shi ne a babban dakin taron Otal din kwamand da ke cikin garin Kaduna.
Mataimakin Gwamnan wanda ya samu wakikcin Umar Muhammed Sarkin Yaki,da ya yi Dogon jawabi ga manema labarai a kan muhimmancin taimakawa marayu abin da ya bayyana da cewa neman tsira ne duniya da lahira.
Wakilin mataimakin Gwamnan ta hannun wakilinsa Umar Muhammed Sarkin Yaki, ya kuma fadakar da jama’a kan irin muhimmancin yin abota da mutum na kwarai ko a matakin gidajen zama ne da kuma matakin kasa da kasa, inda ya bayar da misali da kasar Nijar da Nijeriya.
“Da man can tare kasashen suke in banda a yanzu da wadansu kasashen turawa suka raba kasashen biyu, kusan dukkan yarukan da ke cikin kasar Nijar in an zo cikin Najeriya za a iya samun su don haka ya na da kyau a hada karfi da karfe wato a hada hannu wuri daya kasashen nan guda biyu domin mu fitar da kawunan mu a halin da muka tsinci kai, misali mutanen da ke tayar wa da jama’a hankali akwai su a cikin Najeriya kuma akwai su a cikin Nijar don haka akwai bukatar a hada kai tare a kula da abin da yake tafiya da nufin samun karshen al’amarin da yardar Allah”.
Ya ci gaba da cewa hakan ya Sanya ake samun darussa a Najeriya da harshen Faransanci saboda da yawa ba wai maganar wadancan Nijar ne ko wadannan Najeriya ne ba, A’a akwai wasiyya ma a tsakanin kasashen biyu kowa ya iya yaren kasashen Juna kafin a iya cimma Burin da ake da shi, kuma Gwamnatin Jihar Kebbi matsayinta da ta na a kan iyaka da kasashe ba guda ba duk ana yin la’akari da lamarin.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.