Home / Big News / A Zabi Tinubu Da Uba Sani- Yusuf Kailani

A Zabi Tinubu Da Uba Sani- Yusuf Kailani

 

Daga Imrana Abdullahi
Dan majalisar dokokin Jihar Kaduna daga karamar hukumar Igabi kuma ɗan takarar majalisar dattawa a mazabar Kaduna ta tsakiya honarabul Yusuf Ibrahim Zailani ya yi kira da babbar murya ga daukacin al’ummar Jihar Kaduna da Najeriya baki daya da su sake zaben shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani a karo na biyu domin cimma bukata da nasarar da kowa ke bukatar samu.
Yusuf Ibrahim Zailani, ya yi wannan kiran ne a wajen wani babban taron da aka shirya domin ƙaddamar da biyawa yara dalibai kudin jarabawar fita makarantar Sakandare ta NECO da WAEC da suka fito daga mazabar dan majalisar Unguwar Sanusi a cikin karamar hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna.
Yusuf Zailani ya ce hakika irin yadda jama’a ke mancewa da halayyar wadansu mutane a cikin al’umma abin a duba ne domin halayyar da wadansu mutane ke aikatawa a cikin al’umma abin bakin ciki ne tare da matukar bakin rai, sai ga mutum ko wadansu mutanen da ke gudanar da sana’a suna tauye kudu a wajen gudanar da kasuwancinsu na yin awon kayan abinci ko duk wani abu da suke aunawa mutane wanda hakan lallai ba dai- dai ba ne musamman a wajen gudanar da rayuwar yau da kullum kuma Allah madaukakin Sarkin baya son hakan a rika tauye mudu.
” Akwai dai sauran wadansu abubuwan da addinin Musulunci ya hana da dama amma mutane na aikata su wadanda ko domin saboda su ma za a iya shiga cikin wahalar da ake ciki amma sai kaga wadansu mutane na aikata su ba tare da yin la’akari da fahimtar abin da Yakamata ba.
Saboda haka muna yin kira ga daukacin jama’a da a koda yaushe su rika dubawa suna sanin abin da ya dace su fadi da kuma aikatawa, domin zaka ga waɗansu na zargin shugabannin a wasu lokutan ma sai kaga suna zagin shugabanni kai tsaye ba tare da yin la’akari da yin abin da ya dace ba.
“A nan ina don fadakar da jama’a cewa ba kyau zagin shugabanni ko kadan, ina jama’a ko wani ko gungun wadansu mutane na zagin shugabanni su sani suna yi domin kawunansu ne kuma abu ne mara kyau mutum ya riƙa zagin shugabanni, kai hakan ma na kara jefa jama’a cikin wahala”, Zailani ya tabbatarwa jama’ar da suka taru a wajen taron.
” Ko saboda tauye mudun da ake yi ma kawai zai iya kawo wahala a cikin al’umma, amma sai kaga wadansu na mancewa suna jefa zarge zargen wahalar da suke ciki a wuyan shugabanni ba tare da yin la’akari da abin da suke ciki ba na halayyar rayuwar yau da kullum da za su iya kawo masu wahalar rayuwa”.

About andiya

Check Also

Dangote, Pope Leo XIV, Trump, Xi Jinping, others Named in TIME 100 Most Influential People for 2026

  Renowned African industrialist and philanthropist, Aliko Dangote, has been named among TIME Magazine’s 100 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.