Home / Big News / Auwalu Yaro Mai Kyau Ya Biyawa Dalibai 200 Kudin Jarabawar WAEC Da NECO Karo Na Takwas

Auwalu Yaro Mai Kyau Ya Biyawa Dalibai 200 Kudin Jarabawar WAEC Da NECO Karo Na Takwas

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna arewacin Najeriya
An yabawa Gwamnan Jihar Kaduna Kwamared Sanata Uba Sani bisa irin yadda yake taimakawa ayyukan dan majalisar dokokin Jihar Kaduna Alhaji Auwalu da ake yi wa lakabi da Yaro Mai Kyau da ke wakiltar mazabar Unguwar Sanusi a karamar hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna arewacin tarayyar Najeriya.
Honarabul Auwalu Yaro Mai Kyau ne ya bayyana hakan tare da yi wa Gwamna Sanata Uba Sani jinjina a kan irin yadda yake taimakawa ayyukan da yake yi domin taimakon al’ummar mazabarsa da Jihar Kaduna baki daya.
An dai yi taron ne a dakin taro na makarantar Kwalejin Ahmadu Chanchangi da ke Unguwar Tudun wada cikin garin Kaduna.
Honarabul Auwalu Yaro Mai Kyau ya ce tun farko abin da ya ja hankalinsa game da batun taimakawa yara dalibai su rubuta jarabawar fita makarantun Sakandare shi ne irin yadda ya fahimci tun farko akwai matsalar da ke buƙatar lallai sai an yi irin wannan tallafin.
Daga dama Dahiru Muhammad ne sai a tsakiya honarabul Baban Halima tare da mai gayya mai aiki da jama’ar Mazabar Unguwar Sanusi ke rokon Gwamna Uba Sani cewa su fa ba Canji kawai Honarabul Auwalu Yaro Mai Kyau ya ci gaba da zama dan majalisar mazabar Unguwar Sanusi a majalisar dokokin Jihar Kaduna.
“Babban kalubalen shi ne ita Gwamnati a Jihar Kaduna ta kaddamar da batun yin ilimi kyauta tun daga makarantun Firamare da Sakandare, amma babbar matsalar da ake fama da ita shi ne duk lokacin da aka zo batun fita makarantar ne kalubalen musamman a wurin dan talaka domin na su iya samun yin jarabawar , to, irin wadannan kalubalen ne yasa muka dauki dammarar da duk wata damar da muke da ita domin ganin dan talaka ya samu mafita a wannan bangaren.
Kuma kamar yadda aka sani ana bayar da wannan abun ne a kowace gunduma a cikin mazabar Unguwar Sanusi, saboda haka ne ake kaiwa mutanen da ya dace musamman ma ya’yan da suka kasance marayu hakan ne ya sa shekarar da ta wuce da shekaru kusan Bakwai wannan ta Takwas duk shekara Bama yin mutane kasa da dari biyu, ko a waccan shekarar ma mun yi ma yawan mutane dari Uku ne da wani abu idan an duba muna da dubban matasa ne da suka yi wannan jarabawar kuma Alhamdulillahi muna kallonsa ne a matsayin wani harsashin da su ya’yan talakawan za su zama masu dogaro da kansu.
Saboda a duk lokacin da zaka ba dan talaka ilimi hakika ka gama masa komai duk abin da ka ba shi ka dai ba shi ne kawai amma ilimi shi ne abin da zai taimake shi ya zama wani abu a yaruwarsa don haka ne muke yin godiya ga Allah madaukakin sarki kuma muna yin godiya ga Gwamna Malam Uba Sani wanda da tallafinsa da kuma karfin gwiwa ne muke yin abin da muke yi, muna kara yi wa Allah godiya a koda yaushe.
Sai dan majalisa mai wakiltar mazabar Unguwar Sanusi Auwalu Yaro Mai Kyau ya ce ya na yin kira da jan hankali da daukacin ba wai yan majalisar Jiha da tarayya ba kawai harma da masu hannu da shuni da su gane cewa damuwar talauci da rashin tsaron da muke fama lallai rashin ilimi na daga cikin abin da ke haifar da shi, amma duk idan an samu matasa da ilimi akwai wadansu abubuwan da suke yi na za su yi su ba Sam.
” Masu hannu da shuni ya dace su sani cewa maganar taimakawa dan talaka ya zama mai ilimi kariya ne a wurinsu su kansu don idan mutum zai iya biyawa dansa kudin yin karatu amma dan makyabci ka ba zai iya yin karatun ba to, lallai ba a fatan abin da zai biyo baya domin sune ke addabar wadanda ke da hannu da shunin don haka ayi domin Allah.
” A lokacin da na yi aiki a can baya a matsayin mai bayar da shawara a kan harkokin matasa, na samu nasarar samawa a ƙalla matasa dubu biyu aiki a hukumar kula da ababen hawa ta Jihar Kaduna ( KASTLEA) da sauran wadansu wuraren da dama kuma matasan sun amfana kawai.
Wannan ɗaya ce daga cikin dalibai Mata da suka samu nasarar tallafin jarabawar da aka ƙaddamar domin jama’a su gani a wurin karon karo na Takwas
Sai ya yi kira ga wadanda suka amfana da wannan biyan kudin rubuta jarabawar WAEC da NECO da suka hada maza da Mata da su jajirce wajen yin karatu su sani jarabawa ce za su rubuta da za ta amfane su a koda yaushe domin ita ce matakin ilimin da zai kai su gaba.

About andiya

Check Also

Dangote, Pope Leo XIV, Trump, Xi Jinping, others Named in TIME 100 Most Influential People for 2026

  Renowned African industrialist and philanthropist, Aliko Dangote, has been named among TIME Magazine’s 100 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.