Home / News / A Zamfara Dan Majalisa Ya Rasu Bayan Sauya Sheka Zuwa APC

A Zamfara Dan Majalisa Ya Rasu Bayan Sauya Sheka Zuwa APC

 

Mustapha Imrana Abdullahi

 

Bayanan da muke samu daga Jihar Zamfara na cewa an Sanya karfe Sha daya na ranar yau a matsayin lokacin da za a yi Jana’izar marigayi Honarabul Muhammad G. Ahmed (Walin Jangeru), da ya rasu a jiya da Dare a kan hanyar garin Tsafe dai dai Yan kara Barayi suka harbeshi lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kano, bayan tashi daga taron karbarsu zuwa jam’iyyar APC tare da Gwamnan Zamfara Mohammed Bello Matawalle.

Kamar yadda mai magana da yawun majalisar dokokin Jihar Zamfara ya tabbatarwa wakilin mu cewa Honarabul Muhammad G. Ahmed (Walin Jangeru), ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar mazabar Shinkafi, ya gamu da ajalinsa ne a garin Yan Kara da ke cikin Jihar Katsina sakamakon harbin da barayi suka yi masa ya na kan hanyarsa ta zuwa Kano daga garin Gusau fadar Gwamnatin Jihar Zamfara.

Ya rasu awanni da sauya sheƙa zuwa APC daga jam’iyyar PDP. Yana daga cikin tawagar ƴan majalisun da ta bi gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle suka fice daga PDP.

An bayyana cewa, har zuwa daren jiya yana tare da jama’a a gidan gwamnatin jihar dake birnin Gusau wurin bikin sauya jam’iyyar

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.