Home / Labarai / Abdul Aziz Mai turaka Ya Bayar Da Tallafin Dubu Dari Biyar (500:000)

Abdul Aziz Mai turaka Ya Bayar Da Tallafin Dubu Dari Biyar (500:000)

Abdul Aziz Mai turaka Ya Bayar Da Tallafin Dubu Dari Biyar (500:000)
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarinsa na ganin ya Tallafawa daukacin al’umma musamman ga masu bukatar taimakon Alhaji Abdul Aziz Mai turaka mai ba Gwamnan Jihar Katsina shawara a kan harkokin wayarwa da kan jama’a lokacin wata ziyarar da ya kai domin tattaunawa da kwamitin tallafin Azumi wanda Katsina City news ya assasa domin taimakawa jama’a
A lokacin da ya kai ziyarar Katsina City news ya bayyana jindadinsa da kuma Gansuwa da irin yadda ake tafiya da tsarin tallafin inda nan take ya tallafa da kudi naira dubu dari biyar 500: 000 domin a ci gaba da gudanar da aikin lada musamman a wannan watan Azumi mai alfarma.
Da wannan muke cewa Allah ya saka masa da alkairi ya mayar masa da dubun abin da ya bayar.

About andiya

Check Also

Majalisar Wakilai: Sani Jaji Zai Maye Gurbin Abbas Tajuddeen?

Daga Imrana Abdullahi Kamar yadda wadansu bayanai suka bayyana a kafar yada labarai ta jaridar …

Leave a Reply

Your email address will not be published.