Home / Labarai / ALLAH YA BA NAJERIYA IKON MAGANCE MATSALOLIN TSARO

ALLAH YA BA NAJERIYA IKON MAGANCE MATSALOLIN TSARO

 

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI

WANI JIGO A HARKOKIN SIYASA A JIHAR KATSINA ALHAJI RABI’U LAWAL MASKA DA AKE YI WA LAKABI DA RABE MELA, YA BAYYANA GAMSUWA DA IRIN YADDA SHUGABA MUHAMMADU BUHARI KE KOKARIN GANIN YA WARWARE MATSALAR TSARO A TARAYYAR NAJERIYA.

 

 

ALHAJI RABE MELA, YA BAYUANA HAKAN NE A LOKACIN DA YAKE TATTAUNAWA DA WAKILIN MU TA HANYAR DANDALIN SADA ZUMUNTA NA WHATSAPP.

 

 

INDA YA YI KIRA GA SHUGABA BUHARI DA CEWA YA DACE YA CI GABA DA KOKARIN GANIN AN WARWARE DUK WATA MATSALAR DA AKE FUSKANTA TA TSARO A KO’IN A TARAYYAR NAJERIYA, KAMAR YADDA YAKE BAYAR DA UMARNIN A SHAWO KAN MATSALAR A KASAR NIJAR, HAKIKA HAKAN ABIN A YABA NE KWARAI.

 

 

DA YAKE TOFA ALBARKACIN BAKONSA TSOHON KANSILAN MASKA ALHAJI KABIRU MASKA KIRA YA YI DA CEWA YA DACE A KARA KAIMIN TABBATAR DA TSARON RAYUKA DA DUKIYAR JAMA’A SABODA KO A JIYA SAI DA YAN BINDIGA SUKA JE YANKIN SU SUKA DAUKE WADANSU MUTANE DON HAKA LALLAI YA ZAMA WAJIBI GWAMNATI TA KARA KAIMI TA TASHI TSAJE WAJEN KAWAR DA WADANNAN MASU AIKIN AIKA AIKA A CIKIN NAJERIYA KO JAMA’A SU SAMU SAUKIN GUDANAR DA RAYUWARSU.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.