Home / Kasuwanci / Gwamnatin Jihar Sakkwato Ta Kashe Biliyan 2 A Kan Bunkasa Sana’o’i – Tambuwal

Gwamnatin Jihar Sakkwato Ta Kashe Biliyan 2 A Kan Bunkasa Sana’o’i – Tambuwal

 Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya ce Gwamnatinsa a yan shekarun da suka gabata ta kashe naira biliyan biyu (2) a harkar bunkasa sana’o’i a Jihar.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun  mashawarci na musamman a kan harkokin kafafen yada labarai ga Gwamnan Jihar Sakkwato Muhammad Bello da aka rabawa manema labarai.
An dai kashe kudin ne wajen samawa jama’a manyan sana’o’i da kuma Farfado da wadansu masana’antu a Jihar, duk kuma hakan ya samu ne tare da hadin Gwiwa tsakanin Jihar Sakkwato da Bankin masana’antu an kuma rabawa jama’a kudin bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu a matsayin bashi ga wadanda suka amfana da kudin.
Gwamna Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Asabar Asabar wajen rufe taron bayar da horo ga masu kokarin bunkasa sana’o’insu wanda matasa 130 suka halarta daga cikin Jihar wanda hukumar bunkasa sana’o’i ta Jihar Sakkwato ta shirya da aka yi a babban birnin Jihar.
Kamar yadda Gwamnan ya ce, akwai wadansu karin makudan kudin da suka hada da naira biliyan daya da digo biyar (1.5) da za a bayar da su ga masu karamin karfi da marasa galihu kwanan nan da za a yi gida gida da kanana da matsakaitan masana’antu domin ragewa mama’s radadin da cutar Korona ta haifar.
Kudin da babban Bankin duniya suka samar sakamakon kiran da kungiyar Gwamnoni suka yi domin samawa Jihohi sauki sakamakon illar cutar Korona, duk suna kudin kwanan nan za a rabawa jama’ar da Allah ya ciyar da rabonsu.
“Ina son shaida maku cewa Gwamnatin Jihar Sakkwato tuni ta kammala tabbatar da yin komai game da lamarin kuma nan gaba za a fara aiwatar da aikin kamar yadda yakamata”, inji Gwamna Tambuwal.
Gwamnan ya kara jaddada cewa za a raba kudin ne a matsayin tallafi ga mutane dubu Bakwai da dari biyu da Ashirin da hudu (7,224) a cikin Jihar Sakkwato.
Tsare tsaren guda biyu za a yi sune kamar yadda Gwamnan ya bayyana sakamakon irin rawar da bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu wajen bunkasar tattalin arziki ke takawa da kuma tsarin rage radadin talauci a cikin Jihar baki daya.
Ya ce bayan ga irin yadda aka samu bunkasar tattalin arziki a matakin karkara a Jihar da kuma samawa jama’a da dama aikin yi,lamarin ya kuma taimakawa yan asalin jiha su samu shiga jerin masu Kerawa da kuma masana’antu samar da kayayyaki wanda hakan zai iya jawo hankalin masu zuba jari zuwa Jihar Sakkwato domin yin tsarin hadin Gwiwa.
A jawabinsa, mai ba Gwamna shawara na musamman a kan harkokin bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu na Jihar Sakkwato, Akibu Dalhatu,cewa ya yi an tsara horaswar ne domin kara karfafawa matasa Gwiwa ta hanyar yadda za su san lamarin sadarwa da kuma tsarin bunkasa sana’o’in hannu da nufin samun bunkasar kirkire kirkire.
Jan. 16, 2022
Sokoto

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.