Home / Labarai / Allah Ya Yi Wa Dokta Ibrahim Datti Ahmad Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Dokta Ibrahim Datti Ahmad Rasuwa

 

Mustapha Imrana Abdullahi

 

Bayanin da muke samu daga Jihar Kano na bayanin cewa Allah ya yi wa shugaban majalisar kula da harkokin shari’ar musulunci na kasa (SCSN) Dokta Ibrahim Datti Ahmad Rasuwa an kuma yi Jana’izarsa a Kano.

 

Mai sharkatu 83 wanda kuma Likita ne, ga shi kuma dan siyasa kuma Malamin addinin musulunci ya rasu ne da safiyar yau Alhamis bayan fama da rashin lafiya.

Ya dai rasu ya bar mata daya da yaya 10.

An dai yi Sallar Jana’izar ne a masallacin juma’a na Alfurqan da ke cikin garin Kano , an kuma rufe shi a makwancinsa na makabartar Unguwar Tarauni cikin birnin Kano.

Kamar yadda wani na kusa da marigayin ya bayyana mai suna ABBA Adamu Koki, cewa ya yi marigayin ya yi ta fama ne da matsananciyar rashin lafiya daban daban na kusan shekaru biyu wanda kuma a yau Alhamis Allah ya yi masa Rasuwa.

Abba Koki ya bayyana rashin da cewa na dukkan jama’a ne baki daya.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.