BAYANAN da muke samu daga Jihar katsina na cewa Allah ya yi wa Shaikh Nasiru Sama’ila Ilalla Rasuwa sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Katsina.
Shaikh Nasiru Sama’ila da aka fi Sani na Nasiru Ilalla shahararren Malamin addinin Islama ne da ya yi shura aka san shi a duk fadin Arewacin Najeriya da kuma sauran Jihohin kasar baki daya kasancewarsa matashi mai dimbin ilimin Boko da na arabiyya Sato muhammadiyya.
Wakilin mu ya ce ya san marigayin tsawon sama da shekaru Talatin 30 da suka gabata.