Home / Labarai / Allah Ya Yi Wa Tsohon Gwamnan Legas Lateef Kayode Jakande Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Tsohon Gwamnan Legas Lateef Kayode Jakande Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Tsohon Gwamnan Legas Lateef Kayode Jakande Rasuwa
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo- Olu, ya bayar da sanarwar rasuwar tsohon Gwamnan Jihar Legas Alhaji Lateef Kayode Jakande.
Sanarwar da Gwamnan ya bayar na cewa ina sanar da rasuwar tsohon Gwamnan Jihar Legas da ya kare rayuwarsa wajen yi wa Jihar Legas aiki shugaba abin ko yi tsayayyen dan siyasa, masanin harkokin mulki Gwamnan farko a tsarin farar hula a Jihar Legas Baba Jakande.
Baba Jakande wanda ya kasance dan jarida masanin harkokin aikin kasa na yau da kullum da ya samu nasarori lokacin da ya yi jagorancin Jihar Legas a matsayin Gwamna da ya kafa Harsashin ci gaban da yan baya suke amfana a yanzu.
Hakika rasuwarsa wani babban rashi ne ga kasa baki daya da zamu dade a cikin jimamin abin.
A madadi na da iyalai tare da al’ummar Jihar Legas baki daya ina mika sakon ta’aziyyata ga iyalan,yan uwa da abokan Kwamared Jalande, Allah ya gafarta masa ya bashi Aljannah Firdausi.
“Jakande sarkin aiki”.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.