Home / Idon Mikiya / Al’ummar Jihar Kaduna Sun Koka Bisa Kamawa Da Tsare Kwamandan CJTF Na Kaduna

Al’ummar Jihar Kaduna Sun Koka Bisa Kamawa Da Tsare Kwamandan CJTF Na Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi
A wani gagarumin taron manema labarai da rundunar Civilian Joint Task Force (CJTF) suka kira a babban ofishinsu da ke Rigasa sun koka wa Gwamnatin Jiha, Jami’an tsaro da dukkan masu ruwa da tsaki a kan lamarin tsaro da su Sanya baki domin sakin babban Kwamandan masu aikin kula da harkokin tsaron Dukiya da lafiyar jama’a tare da sasanta tsakanin wadanda suka samu sabani a rayuwa.
Babban Kwamandan Shiyya Usman Abdullahi, ya bayyana lamarin kama wa tare da tsare babban Kwamandan na su a Jihar Kaduna Aminu Sani da ake wa lakabi da “Aminu Bolo”, da cewa lamari ne da ya Sosa wa dimbin jama’ar yankin maza da mata rai sakamakon irin gudunmawar da masu aikin sa kan ke bayarwa wajen ci gaban rayuwar jama’a.
Usman Abdullahi ya ci gaba da cewa ayyukan da suke aiwatarwa domin ciyar da rayuwar jama’a gaba kowa na alasambarka da su domin su na ciyar da jama’a gaba a rayuwarsu.
“Ba a gaya mana laifin da Kwamandan mu ya yi ba kuma shi ma ba a gaya masa abin da ya aikata ba haka kawai aka gayyace shi ya kuma ta fi tare da wadansunmu guda biyu kuma sai aka rike su amma aka yi wa motarsa rakiya har inda ofis din mu yake daga bisa ni kuma aka saki mutanen da aka ta fi da su wajen wata rundunar soja, da muka Sani cewa su ne aka ajiye a unguwar Rigasa, don haka muke son a gaya mana laifinsa saboda mun san ba wanda ya fi karfin Shari’a”.
Usman Abdullahi ya kara da cewa sai da aka zo gidan Aminu Bolo aka yi bincike ba a samu komai ba amma duk da hakan ba a gaya wa kowa dalilin kama shi ba, wanda hakan ya sabawa tsari da ka’ida.
Wakilin mu ya ganewa idanunsa irin yadda al’ummar unguwar Rigasa suka fito domin nuna alhini da goyon baya ga wanda aka kama Aminu Bolo babban Kwamandan na Jihar Kaduna bisa abin da suka kira ayyukansu na amfanar al’umma kwarai.
Mun kuma zanta da wata mata mai suna Linda John da take ta fito ne daga garin Katari can kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ta kuma shaidawa manema labarai irin yadda su kansu ke amfana da ayyukan jami’an sa kan, inda Linda John ta ce akwai wata ranar da yan bindiga suka kwashe mutane a kan hanyar Katari amma Aminu Bolo ya tafi tare da mutanensa suka Kori yan bindigar nan wanda sanadiyyar hakan wasu suka kubuta don haka su na kira da babbar murya a sako Aminu Bolo ko a ina aka tsare shi domin hakan ya sabawa dokar kasa.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.