Home / Labarai / Gwamna Tambuwal Ya Dakatar Da Harkokin Gwamnati, Ya Ziyarci Wuraren Da Yan Bindiga Suka Kai Hari

Gwamna Tambuwal Ya Dakatar Da Harkokin Gwamnati, Ya Ziyarci Wuraren Da Yan Bindiga Suka Kai Hari

 

… Ya Jajantawa Wadanda Aka Kai Wa Harin

– Ya bayyana irin taimakon motoci dari biyar “500” da ya ba hukumomin tsaro.

 

 

Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya dakatar da ayyukan Gwamnatin jahar kacokan a karo na biyu a ranar Alhamis inda ya ziyarci garin Sabon Birni domin yin ta’aziyya iyalan wadanda suka rasa rayukansu mutane 23 a cikin motar Bus da ke dauke da mutane 32 a ranar Litinin.

Tun farko a ranar Larba Gwamna Tambuwal ya gana da dukkanin jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro a jahar Sokoto don sake nazari da fasalta tsarin matakai na magance barazana tsaro da hare haren da yan ta’adda ke kaiwa al’umma a kauyukan jahar Sokoto.

Ranar Alhamis kuma gwamnan tare da ayarin sun kai ziyara gani da ido da yin jaje a wuraren da aka samu wadanan munanan hare haren.

Gwamnan tare da rakiyar mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato Mannir Muhammad Dan’iya, shugaban majalisar dokokin Jihar Aminu Muhammad Achida shugabanin hukumomin tsaro, kwamishinoni, Gwamnan ya ce; “Mun zo ne domin mu jajanta maku sakamakon rashin da aka yi akan wannan rashin adalci da cin amana na yan ta’adda”.

Bayanin ziyara ya nuna irin bakin ciki da kaduwa na Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a kan lamarin tare da neman mafita akan kalubalen dake addabar al’umma.

“Muna addu’ar Allah ya gafarta wa wadanda suka rasa rayukansu ya ba su gidan Aljannah ya kuma ba wadanda suke kwance a asibiti lafiya”. Inji Gwamna Tambuwal

Gwamnan ya yi addu’a ya kuma roki Allah ya ba wadanda suka samu kansu a cikin wannan lamari ikon samun saukin abin da suka gani da idanunsu da ya sanya su a cikin wani yanayi sakamakon harin a cikin sauri.

Ya kuma jaddada cewa “Hakika lamarin wani abu ne mai sosa zuciya irin yadda lamarin ke faruwa a nan da kuma kasa baki daya. A matsayin mu na wadanda Allah ya ba shugabanci a wannan Jihar, hakika mun da mu kwarai da irin yadda wannan lamarin ya faru domin ya ta ba mana zuciya”.

“Ba za mu ta ba yin kasa a gwiwa ba kamar yadda muka yi rantsuwa cewa za mu yi iyakar iyakar mu domin ganin bayan wannan matsalar”.

“Mu na iyakar kokarin mu wajen taimakawa jami’an tsaro da duk abin da suke bukata ba tare da gardama ko daga yatsa ba a Jihar nan, don haka muna mamakin irin wadanan matsalolin.

Mun taimakawa hukumomin tsaro da motoci sama da guda dari biyar, mun kuma bayar da horo ga jarumai na Yan sama da gora da ke aikin sa kai sama da dubu daya wadanda aka tantance aka amince da su”, inji Gwamnan.

Gwamnan ya kuma kara da cewa sun kuma bayar da tallafin Baburan hawa ga masu ayyukan da kai domin su samu saukin gudanar da ayyukansu karkashin sa idanun jami’an tsaro

Domin sama wa wadanda lamarin ya rutsa da su sauki Gwamna Tambuwal ya bayyana samar da tallafin naira dubu dari biyu da Hamsin na kashin kansa ga dukkan wadanda lamarin ya shafa, ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Jihar za ta biya kudin dawainiyar asibitin dukkan wadanda ke a asibiti su na neman lafiya.

Ya ci gaba da cewa za su ci gaba da karfafa ayyukan jarumai da Gora da suke aikin sa kai amma wadanda aka tantance aka amince da su, sabanin irin yadda wadansu kalamai da aka danganta su da dan majalisar Dattawa mai ci yanzu a Jihar cewa an hana ayyukan masu sa kai wato jami’an Bijilante.

da kada su Sanya siyasa a cikin lamarin tsaro, inda ya bayyana cewa a cikin wannan watan na Disamba za a ci gaba da biyan jami’an sa kan kudin tallafi na naira dubu Ashirin ta yadda za su samu sukunin gudanar da aikin na su, saboda haka muna kira ga kowa ya bayar da gudunmawarsa wajen ganin an shawo kan wannan matsalar.

 

 

Da yake jawabin maraba da Gwamna da tawagarsa shugaban karamar hukumar Sabon Birni Honarabul Umaru Danyaro, cewa ya yi “muna godiya da wannan ziyarar jaje da aka kawo mana domin jajen ta’aziyya zuwa wannan wurin sakamakon aikin yan bindiga da satar mutane a shekara daya da ta gabata.

“Jami’an tsaron da ke nan su na bayar da hadin kai da goyon baya ga karamar hukuma. Don haka abin da ya shafi lamarin tsaro damuwar ba ta Gwamnatin Jiha ba ce ta Gwamnatin tarayya ce.

 

 

Gwamna Tambuwal na iyakar kokarinsa. Saboda haka mutane su daina yin korafi na suka ga Gwamnati mai ci a yanzu da cewa kamar ta gaza madadin hakan kowa ya duba yadda zai nemi gafarar Allah game da zunubansa na dai- daiku da kuma na jama’a baki day”, inji Shugaban

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.