Home / Kasuwanci / AN BUDE KASUWAR DUNIYA TA KADUNA

AN BUDE KASUWAR DUNIYA TA KADUNA

 

 

DAGA IMRANA ABDULLAHI

A Kokarin da Gwamnatin da shugaba Muhammadu Buhari ke yi wa jagoranci take yi na ganin al’amura baki daya sun kara inganta Gwamnatin ta jaddada kudirinta na ganin harkokin Noma sun ci gaba da bunkasa domin samun tattalin arziki mai karfi.
Ministan ma’aikatar Noma Dokta Muhammad Mahmud Abubakar ya kara jaddada kudirin Gwamnatin tarayya karkashin Mihamamadu Buhari wajen ci gaba da inganta harkokin Noma da nufin kara Bunakasa tattalin arzikin kasa.
“Tun tali tali an samu nasarar gina tattalin arzikin Najeriya ne ta hanyar yin amfani da arzikin Noman Auduga da Gyada wanda hakan ya bayar da damar samun ingantaccen tattalin arziki da ci gaban kasa tare da al’ummarta baki daya don haka za a ci gaba da ba Noma muhimmanci domin zai iya rungumar jama’a su samu abin yi”.
Ministan wanda ya wakilci shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari a wajen babban taron da aka yi domin bude kasuwar duniyar kasa da kasa karo na 44 ya ce Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bayar da muhimmanci a game da harkar Noma da nufin bunkasa tattalin arziki da kuma wadata kasa da abinci.
Ministan ya ce kamar yadda kowa ya Sani ba a yi wata Gwamnati ba a Najeriya da ta mayar da hankali tare kuma Tallafawa harkar Noma kamar wannan da Muhammadu Buhari yake yi wa jagoranci.
Ya kuma ce Gwamnatin za ta kara matsa kaimi wajen ci gaba da taimakawa harkokin kasuwanci da masana’antu domin kasa ta dogara da kanta a samar da kayayyaki har a fitar da su kasashen waje.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I Rufa’I samu wakilcin Dokta Yusuf Sale daga ma’aikatar bunkasa harkokin kasuwanci da fasahar Kirkire kirkire na Jihar Kaduna wanda ya yi magana mai tsawo sosai a game da ayyuka da kokarinsu wajen bunkasa harkokin kasuwanci a Jihar kaduna.
Inda ya ce har ma Gwamnatin ta samar da wata cibiyar da ta hannanta wa hukumar SMEDAN da Gwambayin tarayya duk da nufin taimakawa jama’a.
Da yake nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambasada Muhammad Nuhu Bamalli, wanda ya samu wakilcin Mahmud Abbas Makama Karami cewa ya yi a koda yaushe akwai tsarin taimakawa masu son kafa kamfanoni a yankin masarautar Zazzau akwai tsarin taimaka masu domin kofa a bude take game da hakan.
Da yake jawabin maraba a cikin wani jawabin da ya yi mai tsawo mataimakin shugaba na biyu na kasuwar duniyar ta Kaduna Mista Ishaya Idi cewa ya yi sakamakon matsalar rashin kara inganta abubuwan da ake samarwa a Najeriya yasa kasar ke rasa dimbin abubuwa da yawa musamman ma biliyoyin naira da ya dace a samu ta fuskar kudin shiga da ciniki.
Shugabar hukumar kula da an yi raba dai dai tsakanin Jihohi wajen daukar ma’aikatan Gwamnatin tarayya Hajiya Farida Muhibbat Dan kaka da sauran dimbin jama’a a ciki da wajen Najeriya duk sun samu halartar taron bude kasuwar duniyar kasa da kasa karo na 44 da ake yi a Kaduna kuma za a yi kwanaki Goma ne ana cin kasuwar da kamfanoni da hukumomin Gwamnati da Jihohi tare da kananan hukumomi za su baje kolinsu a wajen.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.