Home / KUNGIYOYI / KUNGIYAR NOMAN ZAMANI TA NAMCON TA KADDAMAR DA SHUGABANNI RESHEN JIHAR KATSINA

KUNGIYAR NOMAN ZAMANI TA NAMCON TA KADDAMAR DA SHUGABANNI RESHEN JIHAR KATSINA

IMRANA ABDULLAHI
ALHAJI Dokta Aliyu Muhammad Waziri Santurakin Tudun Wada Kaduna ya bayyana cewa manufar kungiyar ita ce su ciyar da baki dayan nahiyar Afrika da wadataccen abinci.
Aliyu Muhammad Waziri ya bayyana hakan ne a wurin bikin kaddamar da shugabannin kungiyar Noman Zamani ta kasa NAMCON reshen Jihar Katsina da aka yi a babban dakin taron tsohon gidan Gwamnatin Jihar Katsina.
Aliyu Waziri ya fayyace cewa a kokarin da suke yi wajen bunkasa tattalin arzikin kasa ya zuwa yanzu sun kaddamar da shugabannin kungiyar NAMCON a Jihohi sama da Ashirin da suka hada da Katsina.
“Zamu dauki tsarin inganta bunkasa rayuwar makiyaya da nufin bunkasa harkar Noman rani a cikin kasa”.
Ya ci gaba da bayanin cewa suna da muhimman ingantattun tsare tsare da dama da za su kara bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya.
Revealing why they established NAMCON in Nigeria the President Comrade Aliyu Muhammad Waziri the Santurakin Tudun Wada Kaduna said they have many projects including NAMCS Super Five (5) that is geared toward empowering people, poverty alleviation, supporting the economic sustainability plan of the federal Government.
“Muna da nufin taimakawa matasan da suka kammala karatu domin su samu abin yi a kasa, saboda akwai mu da tsare tsaren da za su taimakawa Najeriya ta tashi daga kasar da ke zaman shigowa da kayan kasashen waje zuwa kasar da ke samar da kayan amfani a cikin kasar ta”.
Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban kungiyar Noman zamani ta kasa reshen Jihar Katsina Alhaji Abdullahi Maikaita Ummaru cewa ya yi da taimakon wannan kungiya Jihar Katsina za ta cimma wani babban matsayin ci gaban da duk duniya za a yi alfahari da ita, kuma hakan zai Sanya ta ta tserewa tsara”.
Maikaita Ummaru ya shaidawa taron dimbin jama’a maza da mata cewa akwai tsare tsare da dama da suke shirin kawo wa domin kasa ta ci gaba.
Wadanda aka kaddamar dai anmatsayin shugabannin shiyya sun hada da ;
Lawal Inuwa Funtua matsayin shugaba na shiyyar Funtuwa
Usman Umar Daura daga shiyyar Daura
Da Abdullahi Shu’aibu shugaban shiyyar Katsina
Sauran sun hada da Alhaji Shehu Dan Musa, Alhaji Magaji, Alh Abubakar M Doro, Muhammad Saifullahi Safana and Alh Abdullahi Usman dukkansu daga shiyyar Katsina.
Daga shiyyar Funtuwa kuma akwai  Shu’aibu Sa’idu Musawa, Abdullahi Hatuna Musawa, Salisu A Sule Malumfashi and Umar Masari, others are Jafar, Fahad Sama’ila Faskari, Abdullahi Abubakar Dandume.
Daga shiyyar Daura
Bashir Aliyu Sandamu, Bashir Danjuma Mai’aduwa, Musa Salisu, Bala Dahiru, Lawal Halliru, Abdurrashid Sa’ad Mashi, Yusuf Nalado Daura, Ibrahim Sa’id Baure, Abas Mohammad Kankiya and Hamza Hamisu Karfi.
An kuma gabatar da filin yin tambayoyi ko karin haske daga shugaban kungiyar Dokta Aliyu Muhammad Waziri inda mahalarta taron suka rika yi masa tambaya ya na kuma ba su amsa.
Jama’a dai sun bayyana gamsuwarsu da irin kokarin da kungiyar NAMCON take yi domin inganta rayuwar al’umma.

About andiya

Check Also

Sokoto state government dethrones 15 traditional leaders, four others being investigated for various offences

  By S. Adamu, Sokoto Fifteen Sokoto traditional leaders have been dethroned by the Sokoto …

Leave a Reply

Your email address will not be published.