Home / Big News / An Kaddamar Da ALBAYAAN AI Domin Ci Gaban Musulunci

An Kaddamar Da ALBAYAAN AI Domin Ci Gaban Musulunci

Daga Imrana Abdullahi
….Samar Da Na’urar AI: Lokaci ne na Jihadin wannan zamani don haka masu kuɗi su fito su taimaka
….Masu kuɗi su taimaka wajen wannan aikin
Shaikh Dokta Ahmad Abubakar Gumi, ya yi kira ga daukacin al’ummar musulmi baki daya da su fito domin taimakawa wajen samar da na’ura da dandalin sada zumunta na zamani da suka hada da AI da kuma sauran dandalin sada zumunta da nufin amfanar da jama’ar musulmin duniya baki daya.
Na taba tambayar wani da ya san irin wannan manhajar sai na tambaye shi wai me yasa mu ba zamu iya yin wadansu abubuwa kamar su facebook,twitter da sauransu sai ya ce za a iya amma batun shi ne abin da za a kashe wajen samar da kwamfutoci da na’urar sanyaya daki ne matsalar a batun maganar kudi amma da muka duba sai muka ga mutum daya ma zai iya yi.
“Idan aka samar da wannan na’ura ta AI za a samar da ci gaba mai ma’ana da kuma ɗorawar karantarwa ta Da’awa a duniya baki daya.
Muna yin kira ga masu Kuɗi su taimaka
Salisu Hassan da ake yi wa lakabi da (Web master) ya bayyana cewa babban dalilin da yasa suka kirkiro da na’urar bincike ta matambayi baya bata shi ne domin kara karfafa bincike a dukkan lamurran da suka shafi addinin Musulunci ta yadda duk mai gudanar da binciken zai samu abin da ya dace da yake a kan doron ingantacciyar karantarwar addinin Musulunci.
“Ana samun matsalar ƙirƙirar da ba haka take ba ko manhajar AI ta ba mai bincike abin da ya fito daga wani littafi ya ce daga littafi kaza ko kaza yake ko ma ya kirkiro abin da ba haka yake ba saboda a kaucewa hakan ya sa dole muka tashi tsaye domin samun mafita.Hakan ne ya jawo hankalin Malaminmu Shaikh Dokta Ahmad Gumi sai ya yi Mani magana domin samun wannan ALBAYAAN AI da nufin ci gaban addinin musulunci”.
Salisu Hassan ya ci gaba da bayanin cewa fasahar AI wata hanya ce da ake yin amfani da ita wajen abubuwa da yawa,misali zaka iya sashi ya koya maka abu da dai abubuwa da yawa amma shi wannan na ALBAYAAN AI na magana ne a kan abin da ya shafi addinin musulunci da idan mutum ko duk wani malami na yin bincike zai shiga cikin ALBAYAAN AI kawai ya gudanar da bincikensa ya kuma samu abin da yake bukata ba sai ya yi wata wahala ta tara Litattafai ba.
Sai dai Salisu Hassan ya shaidawa manema labarai cewa akwai Kalubale da yawa misali manya manyan Kamfanoni da ba su ma yi abin da muka yi ba suna ta tattara bayanai a gaskiya muna da matsala ta wajen maganar Kudi saboda haka ne muka yi irin wannan ( free lunching) din da aka Tara Yan jaridu,manyan ma’aikatan Gwamnati, masu hannu da shuni da sauransu da su shiga cikin wannan aikin domin a yanzu an yi Gwaji don haka kenan zai iya yuwuwa ayi aikin kuma ya yi abin da ake bukata

About andiya

Check Also

Why Yakubu Dogara Is Claiming Nigeria Is On The Right Track

By Imrana Abdullahi Nigeria is drowning while Rt. Hon. Yakubu Dogara smiles from the comfort …

Leave a Reply

Your email address will not be published.