Home / Labarai / An Karrama Dokta Aliyu Muhammad Waziri

An Karrama Dokta Aliyu Muhammad Waziri

An Karrama Shugaban Noman Zamani Da Lambar “Hasken Matasan Arewa”
Imrana Abdullahi  Kaduna
Sakamakon yin aiki tukuru domin inganta rayuwa jama’a ya sa aka Karrama shigaban kungiyar Noman Zamani ta kasa Dokta Aliyu Muhammad Waziri, da lambar karramawa ta “Hasken Matasan Arewa”.
Taron bayar da lambar karramawar dai an yi shi ne a garin Kaduna, kuma kungiyar matasan Arewa ta (AYCN) ce ta bashi wannan lambar karramawa karkashin jagorancin shugaban kungiyar Tijjani Abdulmumini.
Kamar yadda shugaban tawagar matasan ya ce “hakika shugabancin da Dokta Aliyu Muhammad Waziri ke aiwatarwa abin a ya ba ne kwarai domin ya na sadaukarwa saboda jama’a rayuwarsu ta inganta”, inji Tijjani.
“Sakamakon wannan Namijin kokarin ne wajen ciyar da rayuwar jama’a gaba da shiga jada da kungiyoyi da sauran rukunin jama’a matasa da dalibai ya tabbatar da ka zama abin yin ko yi a cikin al’umma”.
Shugaban na kungiyar na Noman zamani Dokta Aliyu Muhammad Waziri, ya bayyana cikakken farin cikinsa da aka bashi wannan lambar karramawa ta “Hasken Matasan Arewa” inda ya ce hakan zai bashi damar ci gaba da kara yin kokari wajen ciyar da kasa tare da jama’ata gaba.

About andiya

Check Also

The Daily Hug For Appreciation 2023

The daily hug for 28/11/23 is this appreciation of an echo shared by my dear …

Leave a Reply

Your email address will not be published.