Home / News / Cibiyar Tallafawa Manoma Za Ta Kaddamar Da Ko- odinetocinta 44 A Jihar Kano

Cibiyar Tallafawa Manoma Za Ta Kaddamar Da Ko- odinetocinta 44 A Jihar Kano

Mustapha Imrana Abdullahi

Cibiyar da ke rajin Tallafawa manoma ta kasa mai suna “National Agricultural Mechanization Co operative Society” karkashin jagoranci Dan marayan Zaki Dokta Aliyu Muhammad Waziri na gayyatar daukacin al’umma zuwa wajen gagarumin taron  kaddamar da Ko- odinetocinta 44 na Jihar Kano.

Tare da wayar wa da jama’a kai a kan tallafin da Gwamnatin tarayya za ta ba kaso Tamanin (80) cikin dari na mata da kuma Maza a kan kiwon Kaji da karin haske a kan Noman zamani.
Za a yi taron ne a ranar Talata 2 ga watan Nuwamba 2021 a wurin taro na dakin karatu na Jihar Kano da misalin karfe 11 na safe da ke kan  titin Ahmadu Bello cikin garin Kano.

Babban Bako mai girma Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje, mai kaddamarwa mataimakin Gwamnan Kano kwamishinan ma’aikatar Gona Dokta Nasiru Yusuf Gawuna

Uban taro shugaban manoman zamani na kasa Honarabul Dokta Aliyu Muhammad Waziri

Mai masaukin Baki shugaban cibiyar na Jihar Kano Andulhamid Yakubu.

Allah ya bada ikon zuwa amin

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.