Home / Labarai / An Nada Tsohon Mataimakin Gwamnan Katsina, Abdullahi Faskari, Matsayin Sabon Sakataren Gwamnati

An Nada Tsohon Mataimakin Gwamnan Katsina, Abdullahi Faskari, Matsayin Sabon Sakataren Gwamnati

Daga Imrana Abdullahi

Gwamnan jihar Katsina Malam  Dikko Umaru Radda, ya amince da nadin Alhaji Abdullahi Gargba Faskari a matsayin sabon sakataren gwamnatin jiha.

Barista Abdullahi Faskari, wanda tsohon mataimakin gwamnan jihar Katsina ne, tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015, ya maye gurbin  Ahmed Musa Dangiwa, wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabe shi  a matsayin minista.

Gwamna Radda, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, ya ce sabon nadin na Sakataren Gwamnatin Jihar ya fara aiki ne  nan take.

A cewar Gwamnan, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, ana sa ran zai kawo dumbin arziƙinsa na fasaha da kwarewa yayin da ya shiga gwamnatin jihar Katsina.

“Hakika, za a iya kwatanta nadin Abdullahi Garba Faskari a matsayin sabon Sakataren Gwamnati jihar Katsina da cewa wani al’amari ne da ya dace domin haka Allah yaso.

“Gaskiya ya cancanci shiga cikin gwamnatinmu mai son ci gaba, kuma ni da kaina zan iya ba da tabbacin iliminsa da ƙwarewar gudanarwarsa na musamman.

“Dalla-dalla, zai cika girbin  Ahmed Dangiwa da ya zama daga cikin wadanda shugaban kasa ya zaba a matsayin ministocinsa  kuma Sabon Sakataren na daya daga cikin jiga-jigan ma’aikatan jihar Katsina a shekarun baya.

“Gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar da ci gabanta, a lokacin da yake mataimakin gwamna ga tsohon Gwamna Ibrahim Shehu Shema, ba ya misaltuwa,” inji Dikko Radda.

An haife shi a ranar 15 ga Agusta 1959 a garin Funtua, Alhaji Abdullahi Garba Faskari dan asalin karamar hukumar Faskari ne a jihar Katsina.  Tsohon Mataimakin Gwamnan Katsina ya halarci Makarantar Firamare ta Aya da ke Funtuwa a tsakanin 1966 zuwa 1974, sannan ya wuce Kwalejin Malamai ta Dutsin-Ma a shekarar 1974. Bayan ya kammala karatunsa a Kwalejin Malamai a 1980, Alhaji Faskari na neman gurbin karatu ya kai shi Makarantar Koyon Ilimi, a Jami’ar Ahmadu Bello, ABU Zaria, kuma ya kammala a 1983.

Tsakanin 1984 zuwa 1985, tsohon Mataimakin Gwamna ya halarci Makarantar Koyon Ilimi ta Jami’ar Bayero Kano, BUK;  kafin ya karanci shari’a a BUK ya kuma kammala a 1989. Alh.  Garba Faskari ya halarci makarantar koyon aikin Lauya da ke Legas,kuma ya kammala a 1990.

Baya ga samun digirin digirgir (LL.B) (Second Class Upper), Sakataren Gwamnatin Katsina mai shigowa yana da Digiri na biyu (LL.M) da kuma Masta wato digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci wato “Business Administration”(MBA),  Shi mamba ne a kungiyar lauyoyin Najeriya;  Cibiyar Nazarin Gudanarwa;  da kungiyar malaman shari’a ta Najeriya.

Alh.  Garba Faskari tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007 ya kasance babban mai shari’a a jihar.

Kuma Ya sake zama babban Lauya kuma Kwamishanan shari’a a jihar Katsina, tsakanin 2007 zuwa 2009;  Sannan kuma Mai Girma Kwamishinan Ilimi na Jihar Katsina, tsakanin 2009 zuwa 2010. A halin yanzu shi ne Pro-Chancellor kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, da ke Katsina.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.