Home / News / AN RANTSAR DA SHUGABANNIN KUNGIYAR KANSILOLI A KADUNA

AN RANTSAR DA SHUGABANNIN KUNGIYAR KANSILOLI A KADUNA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na Jihar Kaduna Alhaji Abubakar Buba shugaban karamar hukumar Lere ya bayyana kungiyar Kansiloli a matsayin kashin bayan Dimokuradiyya.
Abubakar Buba ya bayyana hakan ne a wajen Rantsar da shugabannin kungiyar Kansiloli ta kasa reshen Jihar Kaduna da aka yi a dakin taro na gidan Arewa cikin garin Kaduna.
Buba, ya ce babban dalilinsa na bayyana kungiyar a matsayin kashin bayan Dimokuradiyya shi ne domin daga nan ne dukkan wata harkar Dimokuradiyya take farawa.
“A madadin shugabannin kananan hukumomi 23 muna farin ciki da murnar kasancewa tare da kungiyar Kansiloli da mambobinta.
Kuma a game da tsofaffin shugabannin kungiyar Kansiloli muna cewa mun gode kuma muna ta ya ku murna kwarai da gaske da sauke nauyin ku.
An dai gabatar da muhimman jawabai tare da gabatar da kasida a kan muhimmancin tafiya tare da jama’a a matakin mazabu, inda aka ja hankalin Kansiloli da cewa su zama wadanda ke tare da jama’arsu a koda yaushe domin samun cimma biyan bukata.
An dai Rantsar da shugabannin kungiyar mutane 30 karkashin shugabancin Honarabul Auwal Sani kansilan mazabar Afaka daga karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
Taron ya samu wakilcin babban Sakatare a ma’aikatar kananan hukumomi ta Jihar Kaduna Alhaji Abubakar Abba wanda ya ta ba zama mataimakin shugaban karamar hukuma a can baya.

About andiya

Check Also

Alleged budget padding : Northern NASS member shun rancour, disunity, to enhance developmental projects 

Kola Kano and Imrana Abdullahi NORTHERN members in the national assembly, have been called upon,not …

Leave a Reply

Your email address will not be published.