Home / Labarai / AN RANTSAR DA SHUGABANNIN KANANAN HUKUMOMI A KATSINA

AN RANTSAR DA SHUGABANNIN KANANAN HUKUMOMI A KATSINA

Daga Abdullahi Sheme
  An yi Bikin rantsar da Mataimakan Shuwagabannin Kananan Hukumomi tare da Sabbin Kansilolin Kananan Hukumomin Dandume, Danja, Faskari da Sabuwa a Jihar Katsina.
A jiya Alhamis ne 14 ga watan afrilu 2022 aka rantsar da sabbin zababbun kansiloli a kananan hukumomin Dandume, Danja, Faskari da kuma Karamar hukumar Sabuwa da ke Jahar katsina.
 Mai Shari’a Shamsudeen Isma’ila ne ya rantsar da kansilolin tare da mataimakan shuwagabannin kananan hukumomin.
Mai Shari’a Shamsudeen ya fara ziyartar karamar hukumar Sabuwa da misalin karfe 12 na rana daga bisani ya ziyarci sauran kananan hukumomin domin rantsar da mataimakan shuwagabannin kananan hukumomin tare da kansilolinsu.
 Tun farko a jawabansu daban daban shugaban karamar hukumar Dandume Alhaji Ya’u Nowa, da na karamar hukumar Danja Alhaji Rabo Tambaya Danja da kuma na karamar hukumar Faskari Alhaji Ado Bala da na karamar hukumar Sabuwa Alhaji Faruk Hayatu duk  sun yi kira ga daukacin  al’ummarsu  da su ba su hadin kai da goyon baya domin samun ciyar da kananan hukumomin gaba.
Sun kuma yi kira ga jama’ar da kowa ya  bada gudunmawarsa don bunkasa kananan hukumomin
kuma sun godewa Jama’a yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana sannan sun godema Gwamnan jahar Alhaji Aminu Bello Masari.
A nasu jawaban shuwagabannin riko masu barin shuwagabannin sashin mulki da kudi na kananan hukumomin watau DAF sun mika ragamar mulki ga sabbin shuwagabannin da  aka zaba Alhaji Idris Ahmed mashi na karamar hukumar Dandume Alhaji Imirana na karamar hukumar Danja da Alhaji Lawal Ibrahim Dan mummuni na karamar hukumar Faskari dana karamar hukumar Sabuwa Alhaji Sani Labo Faskari duk sun yi fatan alkhairi ga shuwagabannin da suka gaje su sannan suka yi kira ga jama’ar kananan hukumominsu su ba sabbin shuwagabannin da suka zaba goyon baya domin ciyar da yankunansu gaba
daga sun gode Gwamnan jahar yadda yabasu damar jagorantar kananan hukumomin Gwamnatin jahar katsina a karkashin jagorancin maigirma Gwamnan jahar Alhaji Aminu Bello Masari ta gudanar da Zaben shuwagabannin kananan hukumomi da Kansiloli na kananan hukumomi 34 dake fadin jahar katsina  a ranar litinin din data gabata 11 ga watan afrilu 2022 kuma tuni Gwamnan jahar Alhaji Aminu Bello Masari ya rantsar dasu a ranar larabar data gabata 13 ga watan afrilu 2022  inda ya umurci shuwagabannin kananan hukumomin su rantsar da mataimakansu tare da zababbun kansilolin su dubban magoya baya da masu ruwa da zaki na jam’iyar APC suka halarci bikin rantsuwar a wasu kananan hukumomin ‘yan majilisun dokokin masu wakiltar kananan hukumomin a zauren majilisar dokoki ta jahar sun halarci bikin rantsuwar irinsu Mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jahar Injinaya Shehu Dalhatu Tafoki mai wakiltar karamar hukumar Faskari da Alhaji Ibrahim Danjuma kaka na karamar hukumar Sabuwa dana karamar hukumar Danja Ciroman Dabai anyi taro lafiya antashi lafiya.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.